ZUNUBAI GUDA BAKWAI MASU HALLAKARWA
*Tambaya*
Assalamu alaikum Mal. wadanne abubuwa ne guda 6 da Annabi yace mu gujesu suna hallakar da dan adam
*Amsa*
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa abubuwan guda bakwai ne kamar yadda suka zo a hadisin Bukhari mai lamba: 6857 da kuma Muslim a lamba ta: 262, inda annabi ﷺ yake cewa: ku guji abubuwa guda bakwai masu hallakarwa:
1. Shirka da Allah.
2. Sihiri
3. katshe rai ba tare da hakki ba
4. Riba.
5. Cin dukiyar maraya.
6. Juya baya a wajan yaki.
7. Yiwa mata katangaggu kazafi.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177