SAHABI JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI!!
Tambaya:
Aslm, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, dansa kuma sahabi?, ina son karin bayani malam?
Amsa:
To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne: Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa: Ba mu san mutum hudu da 'ya'yansu wadanda suka ga Annabi S.A.W ba sai wadannan.
Abin da yake nufi shi ne: Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi S.A.W, don haka su kadai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda.
Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad a Usudul-gabah a lamba ta: 6083.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.