*YA HALATTA NACIRE HIJABI BAYAN IDAR DA SALLAH KAFIN AZKAR?*
Assalamu alaikum
*Tambaya:*
Assalamu alaykum
Dan Allah Malam ya hukuncin maccen da take cire hijabi bayan tayi sallama daga Sallah kuma tayi Azkar daTasbihi batare d ta maida Hijabinba?
Wa alaikumus salam.
*Amsa:*
Azkar dinta yayi domin shari'ar musulunci ta shar'antawa mace rufe jikinta ruf ne a cikin sallah, dan haka in ta idar da sallah babu lefi tacire hijabinta tayi azkar matuqar babu mutumin da ba mahraminta ba a gurin.
*Allah ne mafi sani*
*Amsawa:*✍🏻
*ABDULLAHI ISMAIL AHMAD*
Dan shiga Zauren fiqhul usrah a tura cikakken suna da adireshi zuwaga 08149690671