HUKUNCIN QAYYADE SAQO DA UMURNIN TURAWA WASU ADADI !!!
.
حكم الرسائل التي فيها أرسلهال١٠ أشخاص.
.
العلّامة صالح الفوزان -حَفظَهُ الله-
.
السُّــــؤَالُ:
يقول -حَفظكم الله- في بعض رسائل الجوّال يأتي فيها: "صلّ على النّبي ﷺ وأرسلها مثلًا إلى عشرة أشخاص لتحصل على كذا من الحسنات". فما حُكم فعل ذلك؟
.
الجَــوَابُ:
《هذا بدعة! هذا بـدعة! أصلُ الصلاة على النبيّ مشروع، طيّب، لكن تحديده بعدد وإرسـاله إلى كذا و كذا، هذا بدعة لا دليل عليه. نعم》.
.
________________________________
Hukuncin saqonni (messages) da acikinsu ana cewa turawa mutun goma 10
.
Sheikh saleh al-fauzan [Hafizahullah]
.
Tambaya:
Mai tambaya yana ce wa -ALLAH ya kiyayeka- a wasu saqonni (messages) na waya ana rubuta "kayi salati ga Annabi sannan ka turawa mutum goma misali saboda kasamu lada kaza" miye hukunci aikata haka?
.
Amsa:
(Wannan bidi'ace , asali yin salati ga Annabi shar'antacce ne, tayyib, saidai iyakanceshi dawani adadi da turawa zuwa ga kaza da kaza, wannan bidi'ace batada wani dalili).
.
☆ Tsokaci Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Ya ce: "Duk abinda aka qirqiro bidi'ace dukkan wata bidi'a 6ata ce duk wani 6ata yana cikin wuta"
.
Wannan qirqirarren al'amari yafi yawo a whatsapp, kuma ya kamata Ma'abota Da'awah su dage wajen jan hankalin al'umma domin dai Musulunci bai qayyade adadin mutanen da za'ayiwa nasiha ba balle mutane idan sunyi rubutu su ringa cewa turawa mutum kaza da kaza ko groups kaza ko kuma suce idan baka karanta ba wani abu zai biyo baya da dai sauransu.
.
ALLAH Ya tsare mana imanin mu (Ameen)