*_HUKUNCIN SHAN RUBUTU?_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum malam inada tambaya da Allah menene hukuncin shan rubutu irin Wanda ake rubuta wasu ayoyi sai a wanke a sha.
*Amsa*
Wa'alaikumus salam, To malam ba'a samu hakan daga annabi tsira da amincin allah su tabbata a gare shi ba, haka nan sahabbansa, saidai an rawaito halaccin hakan daga wasu daga cikin sahabbai kamar Ibnu Abbas, ya zo a Zadul-ma'ad "Ibnu Abbas ya yi umarni a rubutawa wata mace mai tsananin nakuda wasu ayoyi na Alqur'ani, don ta samu sauki" haka kuma an rawaito halaccin hakan daga wasu tabi'ai kamar Mujahid, wannan kuma shi ne maganar Imamu Ahmad.
Don haka mutum ya karanta ayoyin shi ne ya fi, domin shi ne ya tabbata a ingantattun hadisai, saidai wanda ya rubuta ya sha ba za'a aibanta shi ba, tun da yana da magabata.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Zadul ma'ad 4\170 da Majmu'ul fataawaa 19\64.
02/12/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.