HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIK

*_HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIK !!!_*

                               *Tambaya:*
Assalamu alaikum, malam jamilu  Idan mutum zai yiwa dan uwansa sallama zai iya cewa Assalamu alaika idan shi kadai ne?.

                                    *Amsa*
Malaman Malikiyya, sun hana cewa Assalamu alaika, saboda ba'a samu hakan daga daya daga cikin magabata ba, kamar yadda ya zo a FAWAKIHUDAWANY

Amma malaman Shafiiyya da hanabila sun halatta hakan, kamar yadda ya zo a Almajmu'u na Nawawy da Kashshaful Kanna'a.
Don han haka abin da ya fi shi ne fadin Assalamu alaikum ko da ga mutum daya ne.

Allah ne mafi sani.

1/1/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)