*_TA AURI WANDA BAYA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU, SHIN ZATA YI IDDA?_*
*Tambaya:*
Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri kanwata, sai daga baya muka gane ya ha'incemu sakamakon rashin mazantaka da baya dashi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne ? don babu wata mu'amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu.
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta: 49 a suratul ahzaab take nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
21 Muharram, 1437
(03/11/2015)
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.