*WAI SHIN ME AKE NUFI DA KYAKKYAWAR CIKAWA?!*
Shehin Malami Shaikh “Khãlid bn Abdirrahmãn Ash-Shãyi'e” Yace:
ﺣﺴﻦ ﺍﻟﺨﺎﺗﻤﺔ ﻫﻮ: ﺃﻥ ﻳﻮﻓﻖ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻗﺒﻞ ﻣﻮﺗﻪ ﻟﻠﺘﻘﺎﺻﻲ ﻋﻤﺎ ﻳﻐﻀﺐ ﺍﻟﺮﺏ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ، ﻭﺍﻟﺘﻮﺑﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﻭﺍﻟﻤﻌﺎﺻﻲ، ﻭﺍﻹﻗﺒﺎﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻄﺎﻋﺎﺕ ﻭﺃﻋﻤﺎﻝ ﺍﻟﺨﻴﺮ، ﺛﻢ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻮﺗﻪ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺤﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ،
ﻭﻣﻤﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻤﻌﻨﻰ ﻣﺎ ﺻﺢ ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ( ﺇﺫﺍ ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻌﺒﺪﻩ ﺧﻴﺮﺍً ﺍﺳﺘﻌﻤﻠﻪ ) ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻛﻴﻒ ﻳﺴﺘﻌﻤﻠﻪ؟ ﻗﺎﻝ : (ﻳﻮﻓﻘﻪ ﻟﻌﻤﻞ ﺻﺎﻟﺢ ﻗﺒﻞ ﻣﻮﺗﻪ)
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ.
→•••MA'ANA:-
KYAKKYAWAR CIKAWA Shine:
Yakasance kafin mutuwar bawa Allah yayi masa Muwafaqa ya datar dashi da (abubuwa kamar haka):
→Nisantar Abinda ke fusata Allah (s).
→Da Tuba daga Zunubbai da Sabon Allah,
→Da Fiskantar Ayyukan Da'a da Alkhairi,
Daganan Sai mutuwarshi ta kasance Acikin wannan kyakkyawan Hali,
Daga Cikin Abinda ke Nuni da Wannan Ma'anar: Akwai Hadisin da ya Inganta daga Anas Dan Malik [Ra] yace:
Manzon Allah s.a.w yace:
“IDAN ALLAH YA NUFI BAWANSHI DA ALKHAIRI SAI YA DAUKESHI AIKI” Sai Sahabbai sukace:
Taya Allah Zai Daukeshi Aiki?
Sai yace:
“ZAI DATAR DASHI DA KYAKKYAWAN AIKI KAFIN MUTUWARSHI”
(Imam Ahmad da Imam Tirmizi Suka Riwaitoshi, Imam Hãkim ya Ingantashi a Mustadrak).
📚علامات وأسباب حسن الخاتمة وسوء الخاتمة ص٣
Allah yayimana Muwafaqa Da Ayyukan Alkhairi Ya Amshi Rayukan mu Akan su!