HUKUNCIN LADANCI A SALLAH

*_HUKUNCIN LADANCI A SALLAH?_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum Malam Meye hukuncin ladanci a sallah haram ne ko in akayi ba laifi ?

                                   *Amsa:*
Wa'alaikum assalam To dan'uwa mutukar liman yana daga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar yadda wasu malaman suka fada.

Amma idan liman yana da lalura ko rashin lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya kasance yana daga murya da kabbara saboda ba'a jin na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito

Allah ne mafi sani.

9/1/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)