YAYA AKE YIN ISTIBRA'I

INA SO NA SAN YADDA AKE ISTIBRA'I ?

Tambaya

Assalamu alaikum, Don girman Allah ina da tambaya ina so na san yadda ake istibra'i da kuma dokokin su. nagode

Amsa
Wa alaikum assalam,

ana yin istibra'i ne da jini daya a zance mafi inganci,yana kasancewa ne ga matar da ta ta yi zina take so ta tabbatar ciki bai shiga ba, kafin ta yi aure, kamar yadda yake wajaba ga baiwar da mai gidanta ya sayar da ita bayan ya take ta ta yi, kafin ubangidan ta na biyu ya fara saduwa da ita, saboda kada a samu cakuduwar nasaba.

Allah ne mafi sani.

Dr, Jamilu Zarewa

 

Post a Comment (0)