HUKUNCIN BAYYANA KARATUN MACE A SALLAH

*_MENENE HUKUNCIN BAYYANA KARATUN MACE A SALLAH_*

Assalamu alaikum.

Malam ina da tambaya, kamar wurin da ake bayyana karatu a sallah, ita ma mace zata bayyana ne????

*AMSA*

Wa'alaykumussalam

Toh a mazhaba na malikiyya:-
''Mace bazata bayya karatun sallar ta ba, zata yine a asirce gwargwadon yadda zata jiyar da kanta"

Amma malaman hadisai sunce:-
''Babu laifi ta bayyana,kamar yadda namiji yake bayyanawa, suna kafa hujja da hadisin manzon Allah, inda yake cewa: ''Kuyi sallah kamar yadda kuka ganni ina sallah"
  Sai suka ce, wannan umarnin ya shafi maza da mata.

Don haka dai,babu laifi inta bayyana kamar  maza(a inda ake bayyawa, in kuma ta asirta to shima babu laifi, domin akwai fatawar magabata.

Wallahu A'alam

*_Malam Nuruddeen Muhammad Mujahid_*

Post a Comment (0)