ZANCEN BATSA TSAKANIN MASOYA

*ZANCEN BATSA TSAKANIN MASOYA ! ! !*

*Tambaya*

AssalamuAlaikum.
Wai shin menene hukuncin saurayi idan suna hira da budurwarsa sai ya dinga yi mata hiran matar aure? , yana ce mata sha'awa tana damunsa, ita kuma budurwar ba bazawara ba ce, dan Allah mei matsayin hiran a shari'a? Allah ya kara muku Basira da ikilasi

*Amsa*
Wa alaikummussalam.

Bai dace saurayi ya dinga zancen sha'awa ba ga matar da bai aura ba,Tun da Shari'a ta haramta yasashshen zance a aya ta : 3 a Suratul Muminun, kuma hakan yana iya kaiwa zuwa ga zina, idan aka samu macen da ba natsatstsiya ba, ko kuma Shaidan ya ratsa, Yana daga cikin manyan ka'idojin sharia toshe hanyar da take kaiwa zuwa barna.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Zarewa*

22/1/2016

Post a Comment (0)