IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BAYA KOMAWA

*IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BA YA KOMAWA !!*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam wata baiwar Allah ce suka sami sabani da mijinta sai yabita inda take aiki yaje yana nemanta sai tafadama wata agurin taje tacemai batanan sai mijin yace d yar sakon tace yasaketa saki uku kuma itama taji da kunnenta,sai daga baya yace shi be saketa b shine tace atambaya mata ta saku ko aurensu nanan tunda ba ita yafada ma ba.Nagode
*Amsa*
Wa alaikum assalam,
Ta saku mana tun da saki ba'a wasa da shi in har ya fito daga baki ko da wasa ne ba ya komawa, musamman kuma wacce aka yiwa sakin ta ji da kunnanta, ai karya ta kare.
Inkarinsa ba zai yi amfani ba, tun da an tabbatar ya furta.
Don neman karin bayani duba: Zadul-ma'ad 5/204.
A mazhabarmu a Malikiyya ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da saki uku A kalma daya Bidi'a ne, kuma haka ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na zamanin Umar RA, kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan
Allah ne mafi sani.
*Dr, Jamilu Zarewa*
16/09/2017

Post a Comment (0)