BAKIN ARTABU 3 B

***★BAKIN ARTABU**cigaban
**JARUMA*YAZILA★***
Littafi Na Daya {3}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
==============================
=============================
Sarki uhaisu yaci gaba da duru-duru kawai sai ya falfala da gudu koda dakaru suka ga yana gudu sai suka bishi sarki uhaisu yana cikin gudu a gidan sarauta kawai sai ya hango wani mumbari mai tsayi sai yai sauri ya ya goya dabira a bayansa ya daka tsalle ya hau kan munbarin yana hawa ya kara daka wani tsallen sai gashi ya haure katangar gidan sarauta koda masu gadin kofar birnin suka ganshi goye da jaruma dabira sai suka bishi aka kasa tsere.
Al'amarin sarki uhaisu kuwa lokacin da ya kama azababben gudu goye da jaruma dabira a bayansa wadannan dakaru masu gadin kofar na biye dashi amma sai suka kasa cimmasa domin tazarar da yabasu bakadan bace.
Koda suka ga baza su iya cimmasa ba sai suka fara zaro kibiyoyi suna danawa suna kai harbi.
Sai da suka shafe rabin sa'a suna gudu su basu cimmasa ba shi kuma bai bace musuba. Ana cikin hakane wani acikin dakarunnan mai shegen naci yasamu nasarar harbin sarki uhaisu akafarsa ta hagu
Koda kibiyar ta sokeshi a sangalelen kafarsa ta faso nama ta fito jini yai tsartuwa sai sarki uhaisu ya tsandara ihu sakamakon tsananin zafi da zugi da yaji amma saboda tsananin juriya da jarumtaka bai fadi ba kuma bai tsaya ya zare kibiyar ba, yaci gaba da gudu a hakan, maimakon ma ya sare sai ya sami karin kuzari da karfin gudun nasa ya kara tsananin tamkar iska ce ke kara shi gaba. Nan da nan cikin kankanin lokaci ya sake baiwa dakarun tazara mai yawan gaske ya bace musu bat da gani.
Haka dai sarki uhaisu yaci gaba da falfala gudu har sai daya bar cikin daji ya nausa ya sake yin tafiya mai nisa ta tsawon kimanin sa'a uku a sannan ne jiri ya fara dibarsa saka makon. Jinin dake zuba a kafarsa.
Kawai sai ji yayi ya yanke jiki ya fadi kasa da ruf da ciki a matukar galabaice a sannanne ya samu ya kwance dabira daga bayansa ya shimfideta a gefe sannan ya dubi kibiyar dake nutse a cikin kafarsa, ga jini na zuba kawai sai takaici yarufe shi sakamakon tunowa da cewa soyayyace ta janyo masa wannan kaskancin a matsayinsa na sarki mai cikakken iko kuma sadaukin jarumi mai dakawa maza gumba ahannu, wanda bai taba guduwa ba a filin daga balle ya ja dabaya.
Nan da nan sarki Uhaisu ya mike tsaye da kyar yaje ya samo kiraren wuta da kyastu ya hada wuta sannan ya sanya wuka a cikin wutar domin ta gasu tayi jajir. Sai da wukar ta gasu ainun sannan yasa hannu ya zare wannan kibiya daga cikin kafar
sa farat daya cikin zafin nama aikuwa sai ya sake tsandara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugi.
Cikin dauriya ya dauko wannan wuka ya dodanata akan ramin raunin da kibiyar tayi masa ya soye, ya ci gaba da ihu har ya gama soye raunin duka. A sannan ne kuma ya sake mikewa tsaye ya tafi neman ganyen wata bishiya.
Cikin sa'a ya samo ganyen da wuri ya dauko ya dawo inda dabira ke kwance ya zauna ya dandaka wannan ganye ya shafashi akan raunin kafar tasa don kada kunar ta tashi ta zama ciwon kuna.
Faruwar hakan keda wuya sai Dabira ta farka. Koda ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin daji kuma taga sarki Uhaisu zaune agabanta yana yimata murmushi sai ta doki kirjinsa da kafarta ya hantsila baya ta falfala da azababben gudu. Aikuwa sai yamike zumbur! Ya bita da gudu. Kafin cikar dakika biyar ya kure mata gudu ya sha gabanta. Nan fa suka kaure da fada ta rinka kai masa bugu da naushi da dukkan karfinta shi kuwa ya rinka kare dukkan hare-haren nata ba tare da ya maida mata martaniba.
Koda ya ga tana neman ta cutar da shi sai ya nuna mata tsagwaron karfin damtse gami da fifikon kwarewa ya sureta sama ya damfarata da kasa ya danneta da ruf da ciki ya murde hannayenta duka biyu a bayanta. Ya dauresu ta mau da yankin nan wanda ya goyata da shi abaya sannan ya tasheta zaune shima ya zauna suka fuskanci juna tana harararsa shi kuma yana yimata murmushi. "
Cikin murya mai taushi sarki uhaisu ya dubi dabira yace, "Ya ke ma'abociyar kyawu kiyi sani, cewa ban kawoki nan domin na cutar dakeba sai dan kamuwa da tsananin kaunarki da zuciyata tayi idan kika yimin alkawarin bazai sake yunkurin guduwaba kuma bazaki cutar daniba zankwance ki yanzunnan.
Ina son ki bani soyayya ta gaskiya kamar yadda zuciyata ta kamu da tsaninin sonki domin na kaiki birnina ki zama sarauniyata kuma abokiyar rayuwata ta har abada"
Koda sarki Uhaisu yazo nan azancensa sai dabira ta tofa masa yawu a fuskarsa tace, "Har abada babu soyayya da amana tsakanin ruwa da wuta.
Ka sani cewa ni musulmace, kai kuma kafirine don haka mun zama hannun riga babu ta inda zamu iya zama tare.
Na rantse da girman Ubangijinaa bazan taba baka irin soyayyar da kake bukataba.
Ina mai shawartar ka da ka kwanceni kuma ka sakeni na koma izuwa ga birnina kuma ka cire soyayyata daga cikin zuciyarka domin zai fiye maka alheri. "
Sa'adda dabira tazo nan a zancenta sai sarki uhaisu ya kamu da tsananin bakin ciki gami da takaici har ya daga hannu zai mangareta sai ya kasa ya kura mata idanu kawai a lokacinda kwallar ta kaici tazo masa ya tuna cewa tunda uwarsa ta haifeshi yazo duniya ba a aba tofa masa yawu a fuskaba sai yau. Shin dama haka soyayya take, kana son mutum amma kuma shi ya tsaneka?". Sarki uhaisu ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Lokacin da Dabira taga sarki uhaisu ya kura mata idanu har kwallar takaici ta cika masa idanuwa sai tausayinsa ya kamata taji kamar ta gaya masa gaskiya cewar ba ita bace gimbiya yazila wacce ya kamu da tsananin sonta amma sai wata zuciyar ta haneta sarki Uhaisu ya mike tsaye ya koma gefe daya ya tsaya yana tunanin abin da zai fishsheshi.
Kawai sai yaji dabira tace, "Nifa kishirwa nakeji".
Koda jin wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya fashimci cewar babu ruwa a kusa kuma gashi dare ne sosai ga tsananin duhu a cikin dajin amma kuma sai yaji cewar ba zai iya barinta da kishirwa ba dole ne ya je ya samo mata ruwan.
Kawai sai ya taho gareta da nufin ya kamata ya goyata a bayansa su tafi neman ruwan amma sai ta dakatar dashi da hannayenta tana mai daka masa tsawa tace, "Kai mufa a addininmu haramunne na mijin da ba muharraminka ba ya taba jikinka.
Daga yau kada ka sake kusantata, kawai ka kwance mini hannayena na taka da kafafuna mu tafi neman ruwan tunda yanzu ko ka kyaleni kayi bazan iya komawa birninmu ba domin kaina ya juye ban ma gane a ina nake ba yanzu kuma ga tsananin duhu a wannan daji zan iya fadawa cikin wani wurin dazan iya cutuwa ko na hallaka".
Sarki Uhaisu ya dubi dabira cikin alamun rashin yarda yace, "Menene tabbacin cewar idan na kwanceki bazaki cutar dani ba kuma bazaki gudu ba?"
Dabira tayi dan guntun murmushi a gareshi tace, "Na rantse da girman ubangijina bazan guduba kuma bazanyi yunkurin cutar dakaiba bisa sharadi guda sharadin kuma shine ba zamu rinka kwanciya a waje daya ba daga nan har muje birninka kuma zaka kyaleni na rinka yin ibadata".
Koda jin haka sai sarki Uhaisu yayi murmushi yace, "Ai wannan mai saukine, na yi alkawari duk zan yi kamar yadda kika bukata".
Koda gama fadin hakan sai sarki Uhaisu ya kwance hannayen Dabira daga daurin da yayi mata ya dubeta ya ce, "Na san cewa kuna kiyaye darajar Ubangijinku da girmansa don haka na yi imanin baza ku rantse da shi ba kuma ku saba alkawarin, shi yasa na amince na kwanceki yanzu sai kizo mu tafi neman ruwa".
Koda gama fadin hakan sai ya dauki ice daya daga cikin kiraren nan daya kunna wuta sannan ya nannadeshi da yankin nan na damararsa ya cinna wuta ya rikeshi a matsayin fitila dazata. Haska musu hanya ka wai sai ya nausa daji take dabira ta bishi a baya da sauri, sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna neman ruwa basu samu ba sannan suka riski wata korama wacce ruwanta ke zubowa ta kan saman wadansu duwatsu. Ruwane garai-garai har wani irin kamshi yake mai dadi.
Cikin matukar farinciki Dabira da Uhaisu suka ruga izuwa bakin kooramar suka tsugunna suka sha sannan suka dawo gefe suka zauna.
A sannan ne wata irin iska mai tsananin sanyi ta fara kadawa wacce tasa jikinsu ya kama karkarwa kawai sai dabira ta dubi sarki Uhaisu a fusace tace, "Ya za a yi ka baroni da gidanmu inda na saba kwanciya a cikin daki kuma akan shimfida mai taushi kakawoni nan cikin daji inda sanyi ma zai iya lahantani?
Hakika ka zalunceni kuma ka cutar da ni. Haka ake yin SOYaYYA ka cutar da masoyinka?"
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Uhaisu ya dugunzuma ainun ya dubi dabira cikin alamun tsananin da muwa yace, "KI gafarceni ya masoyiyata yanzun nan zan magance miki wannan sanyi da ya dameki".
Yana gama fadin hakan ya mike tsaye yaje ya kama saran bishiya sai da ya karyo rassa dogaye da masu kauri da yawa sannan yazo ya shiga aikin gina daki. Har ya kammala ginin dakin da itatuwa ya lullubeshi da ganye Dabira na zaune tana kallonsa kawai tana mamaki.
A zuciyarta tana cewa, "yanzu kawai saboda ya kamu da soyayya yake ta wahala yake ta wahalar da kansa haka? Lallai kuwa ashe gaskiyar masu iya magana da suka ce "SOYAYYA dafice wacce in ta shiga jikin mutum bata fita har ajali"
Bayan sarki Uhaisu ya gama gina dakin ice har da kofarsa ta shiga sai kuma yaje ya nemo ganyaye masu fadi da taushi yazo ya yiwa Dabira shinfida dasu a cikin dakin sannan yace ta shiga cikin dakin ta kwanta shi zai tsaya. A waje yayi gadin ta don kada wata dabbar daji tazo ta cutar da ita".
Ba tare da gardamar komai ba kuwa dabira ta shiga cikin dakin ta turo kofa ta rufe tayi kwanciyarta ba tare da ta sake jin wani sanyi ba. A sannan ne fa taji tausayin sarki Uhaisu ya kamata domin ta san cewa ba karamar wuya zai shaba idan ya kwana a filin allah cikin wannan tsananin sanyin.
Saukinsa daya ya hura wuta wacce zai rinka jin dumi, kuma koda wutar barci dai bazai yiwuba a wajensa kuma wannan sanyin zai iya cutar dashi.dabira taji kamar ta tashi ta bude masa dakin tace ya shigo amma data tuna cewa abune mai hadarin gaske a addinance ta kwanta da. Wani da namiji a cikin dakin sai ta fasa.
A suba nayi Dabira ta farka daga barci ta bude dakin ta fito waje domin tayi alwala. Tana fitowa taga sarki Uhaisu zaune a gaban wuta yana jin dumi amma jikinsa na ta karkarwar dari kuma idanunsa sunyi jawur sakamakon rashin samun barci.
Nan take taji tausayinsa amma sai ta murtuke fuska ta kau da kai ga barin kallonsa taje bakin wannan korama ta tsugunna tayi alwala sannan ta mike tsaye ta fuskanci alkibla ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallar ne ta shiga yin addu'o'I bata gushe ba tana yin addu'o'in har sai da alfijir ya keto gari ya fara haske sannan ta shafa addu'ar ta waigo ta dubi sarki Uhaisu tace, "Menene abin yi yanzu?
Zaka nemo mini abincin kalaci ne ko kuma zamu ci gaba da tafiya ne?"
Uhaisu ya dubeta cikin alamun damuwa yace, "Ki gafarceni ya masoyiyata bai kamata mu tsaya yin kalaciba anan domin ina zargin cewa mutanenku sun biyo sawummu, gwara mu kara gaba muyi nisa tukunna sai mu yada zango na nemo mana abincin kalaci".
Ba tare da gardamar komaiba Dabira tace, "Na amince da hakan".
Nan take suka hada nasu-inasu suka bar wannan daji suka kara gaba.
Babban kuskuren da sarki Uhaisu yayi shine da bai rushe wannan daki daya gina ba kuma bai batar da ragowar wutar daya kunna ba domin sun zamo alama ta cewar suna cikin wannan daji shida gimbiya Dabira.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Uhaisu da gimbiya Dabira bayan ya satota daga gidan sarutar sarki Raihan a matsayin masoyiyarsa Jaruma YAZILA wacce ya kamu da tsananin kaunarta kuma yake son ta zamo abokiyar rayuwarsa ta har abada.
==============================
=============================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani

Post a Comment (0)