DAREN KA NA FARKO A KABARI

[TUNATARWA Darenka Na Farko A

Cikin Kabarinka 'Dan uwa, duk abinda za ka karanta din nan babu tatsuniya ko kokwanto a cikinsa. Zauren Fiqhu ya tattaro bayanin ne daga Sahihan Hadisai na Manzon Allah (SAW) wadanda Manyan Malamai suka tattaro a cikin litattafansu. Darenka na farko a cikin kabarinka shine dare mafi razani da firgitarwa daga cikin dukkan darare.. Hakika tun lokacin da suka zo suka binne ka, Idan sun ajiye ka a gefen kabarinka, Shi kansa kabarin zai yi magana da kai. Zai tambaye ka shin me kake gani a cikinsa? Za ka ce masa ai babu komai. Shi kuma zai ce maka, to duk abinda ka gani na alkairi ko sharri, to kai ne ka zo da abinka!!! Idan kai mutumin banza ne mai bin son zuciyarsa, mai biyewa sha'awarsa, to Shaidan ya riga ya san ya gama da kai. Don haka zai zo gefen kabarinka yana yi maka dariyar mugunta.. Idan kuwa ka zamanto mutumin kirki mai tsoron Allah, mai halayen kirki, to tun daga mutuwarka Shaitan zai rika tsula kuka da ihu wai saboda bai samu damar dulmiyar da kai cikin hallaka ba. Idan sun gama binne ka, Allah zai dawo maka da ruhinka cikin jikinka. Nan take za ka rika jin maganganun 'Yan uwanka amma babu damar ka amsa musu. Kana jin takun takalminsu amma babu damar ka tashi ka bi su. Idan kai Mumini ne cikakke, Nan take za ka ga wasu Mala'iku farare masu kyawawan kamanni za su shigo har cikin kabarinka. Za su yi maka sallama sannan su zaunar da kai su tambaye ka : "WANENE UBANGIJINKA? MENE NE ADDININKA? KUMA MAI ZA KA CE GAME DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW) - Za su nuna maka siffarsa" Za ka ba su cikakkiyar amsa: "Allah ne Ubangijina, Musulunci ne addinina. Kuma Annabi Muhammadu (SAW) Shi ne Manzona na yi imani da shi. Shine ya isar min da sakon Ubangiji". Nan take Mala'ikun za su yi maka kyawawan kalamai. Za a nuna maka gidanka na Aljannah kuma za a bude maka wata kofa wacce ta nan ne ni'imomin cikinta za su rika shigo maka har zuwa ranar tashin kiyama. Idan kuma Kafiri ne ko Munafiki (mai imani abaki, amma zuciyarsa babu soyayyar Ma'aiki SAW) Ko kuma mai bin son zuciyarsa, a wannan lokacin zai ga wasu Mala'iku bakake masu mummunar kamanni.. Za su shigo har cikin kabarinsa, su tashe shi su zaunar da shi sannan su tambaye shi "WANENE UBANGIJINKA? MENE NE ADDININKA? KUMA ME ZA KA CE DANGANE DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW)? Zai ce "Aah!! Aah!! Ban sani ba! Ban sani ba!!" Sai Mala'iku su fara jibgarsa da wata irin gudumar bakin karfe wacce ba za ta misaltu ba. Idan ya kwarara ihu sai dukkan halittu sun ji shi. In banda mutane da Aljanu. Wannan ranar tana nan zuwa gare mu baki daya. Da ni da kai, da ke, da ku, duk sai mutuwa ta riske mu.. Kuma sai mun yi kwanciyar kabari.. Kuma sai an tambaye mu akan ayyukanmu. Shin sau nawa kake tuna wannan ranar a kullum? Shin kana yin tanadi domin zuwanta? Ko kuma tanadin gyaran duniyar ka kawai kake yi? Ya Allah afuwarka muke kwadayi, Rahamarka muke roko, Falalarka muke sa rai.. Ya Allah ka gafarta mana ka gafarta ma Iyayenmu da Malumanmu da iyalanmu da dukkan Musulmai maza da mata. Da fatan duk wanda ya gani zai taimaka ya tura domin fargar da al'umma saboda su karu. KA TUNA DA DAREN FARKO A CIKIN KABARINKA!] is good,have a look at it! https://mbasic.facebook.com/story.php?story_fbid=1582113605236667&id=100003141285691&_rd
r

Post a Comment (0)