TAMBAYA TA 2,862

*Asssalamu Alaikum* . . *Tambaya ta 2,862:* = Kalmar da ake cewa kama tu dini tudan wai kagota akayi wai babu inda akace duk abinda kayi sai anyima wai fadace kurin irinta mutane Sannan kuma wai da akace mazinaci abokiyar auranshi yar uwarshi mazinaciya wai shima karyane Dan Allah inaso ayimin Karin haske akan wannan tambayoyin nawa = = Amsa = = _Toh wannan kalmar ta cewa duk abinda kayi sai anmaka irinshi to wannan lafazine na wasu daga cikin magabata amma ba hadisi bane na Annabi (s.a.w) tabbatacce, Aa maganace ta masu hikima kuma sun ginatane akan wadansu hadisai wanda Annabi (s.a.w) musamman wanda yake cewa kuzowa mutane ta hanyarda kukeso suzo muku****_ _Amma dai a takaice ba sharadi bane cewa dole dole duk abinda kayi sai anmaka irinshi, wannan maganar waqi'i ma ya sa6a mata domin mutane dayawa sun aikata alheri an aikata musu sharri, hakanan wasu sun aikata sharri an aikata musu alheri, dan haka waccan maganar ba sharadi bace sannan kuma wata rai bata daukar alhakin abinda wata rai tayi****_ _Cewa kuma mazinaci abokiyar aurensa mazinaciya, ni banma taba jin wannan maganarba seyau dan haka bansan gaskiya ko karyartaba****_ _Sedai ina kyautata zaton cewa waccan ayar suke kokarin fassarawa amma basu fahimcetaba kuma basubi fassarar magabata ba, Amma ita ayar abinda take cewa shine: Karuwa, duk mace wacce agarinsu akasanta cewa karuwace zina shine aikinta to wannan matar bai halasta wani ya auretaba face Namiji irinta bansan yaya ake kiran karuwan namiji da hausaba, wato wanda shima ya shahara da zina ansanshi akanta kamar yadda akasan waccan matar to shine kawai yake halasta ya aureta domin mutumin banza sai irinsa*****_ _Amma ba daidai bane dan ansamu wata mace shaidan ya ribaceta ta aikata zina shikenan semu hukunta waccan ayar akanta, Aa bahaka ake nufiba, domin babu wani ma'asumi kowa yana iya yin kuskure dan mutum talala6iya tasameshi yasha giya sau daya ko biyu ba dogewa yayi akan shan giyaba wannan baka kiranshi da sunan dan giya, hakanan wanda yayi sata kawai seka koma kana kiransa barawo bayan kuma satarnan sau daya yayita ko sau biyu amma ansan ba aikinsa bane, to hakama wacce shaidan da sha'awa sukasa tayi zina amma ba,a santa da halin banza ba wannan baka cemata karuwa kuma waccan ayar ba da irin wannan macen takeba, Aa ana maganane akan karuwa wacce ta doge akan zina, kai itama kanta karuwar idan tatuba Allah yace yayafe mata limamin jumu'a ma ya halasta ya aureta ababin halasci bawai wajabciba, dan haka jama'a muyi kokari mu rika fahimtar ayoyin qur'ani ta hasken fassarar magabata****_ = = Allah Yasa mudace . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . *مجلس تعليم الكتاب والسنة* 📓📔 Watsaps 08036222795 09031200070 . . Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ . ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. . Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
Post a Comment (0)