TAMBAYA TA 48

TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum sheik jamilu gumil allah ya karawa babban malaminmu lafiya da sawanrai amen allah ya kara ilimi da basira allah ya yasa agama duniya lafiya amen inadatambaya anan shine naji wani yatam bayika gameda mutu zai tashi mai makon yace mismilla sai yace ya ladihu ko yace yaazizu ko yace ya annabi toh ina so afahimtarda ni gameda wannan abun allah ya bada ikon amsa wa 👂👂👂👂 AMSA ====== 👇 Sabida manzon Allah saw ba haka yake fadi ba a wannan wurin. Kenan bismillah yake yi. Tinda haka yakeyi, kaima ya zama wajibi haka zakayi. Misali, idan akazo za'a sa mutun a kabarinsa, sai Kaji wasu sunce LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADURRASULULLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM, kaga duk duniya babu abinda ya kai wannan kalmar, kamar yadda hadisai sukazo mutawatirai daga manzon Allah saw, sannan da furta wannan kalmar ne wanda ba musulmi ba yake zama musulmi, amma manzon Allah saw lokacin da akazo sanya mamaci a kabarinsa bai fadeta ba, duk da cewar yafi kowa sanin matsayin wannan kalmar. Abinda wasu mutanen basu gane ba shine, shi addini na Allah ne ba Naka bane ba nawa bane, haka ba'ace kowa yayi yadda ya gadama ba, Sabida haka yadda manzonsa yace haka za'ayi. Ba kari babu ragi babu tahrifi. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)