KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 02

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 02
.


Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa 
.
                     TA'ALIƘI (I)
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu, da alayensa da sahabbansa, da duk waɗanda suka biyo bayansu da yin koyi da su har zuwa ranar tashin ƙiyama, amin.
.
Bayan haka, na duba wannan littafi mai suna: "Kafofin Sadarwa Na Zamani A Mahangar Addinin Musulunci" wanda Malam Aliyu Muhammad Sa'id Gamawa ya rubuta. Babu shakka marubucin wannan littafi ya yi ƙoƙari matuƙa, na yaba da wannan littafi, littafin ya amsa sunansa, kuma ya dace da abin da musulmi ke buƙata a yanzu.
.
Duba da irin rawar da kafofin sadarwa na zamani ke takawa a rayuwar al'ummar wannan zamani. Littafin ya mayar da hankali ne wajen bayyana irin abubuwan amfani da waÉ—annan kafofi na sadarwar zamani suke É—auke da su da hanyar da ya kamata a bi wajen samun ribatar wannan amfani.
.
Sannan kuma a gefe guda littafin ya bayyana irin ɗimbin illolin da waɗannan kafofin na sadarwar zamani ke da su, tare da ba da ingantattun shawarwarin yadda za a yi ƙoƙarin kaucewa waɗannan illoli bisa mahangar addinin musulunci.
.
Din haka ina ganin ya dace ga dukkan musulmi ya mallaki wannan littafi domin amfanuwa da ilimin da ke cikinsa. Daga ƙarshe, ina roƙon Allah ya saka wa wannan malami marubucin wannan littafi da alheri. Allah ya amfanar da dukkan musulmi da wannan littafi, ya sa ya zama sanadin gyaruwar halayyar al'ummar musulmi na wannan ƙasa tamu da sauran ƙasashen musulmi na duniya. Amin.
.
ÆŠan'uwanku
Nura Musa Abubakar
nuramuaa176@gmail.com
Post a Comment (0)