TAMBAYA TA 49

TAMBAYA ======== 👇 slm Da fatan Mallam yawuni lafiya Allah ya kara basira, tambayata itace in mutun yana Neman auren mace ya hallarta ya ganta sanyi da sutura tamutunci amma babu gele koh hijab? AMSA ===== 👇 To anan Malamai sunyi sabani wajen kallon matar da zaka aura. Duba da hadisin da manzon Allah saw yake cewa, IDAN SON WATA YA SHIGA ZUCIYAR DAYANKU KUMA YAKE SONTA DA AURE, SAI YAYI KULLI ABINDA ZAIJASHI GA SONTA KO AURENTA. Da Wannna ne Malamai suka sami sabani akan cewar ina ya kamata mutum ya gani a jikin matar sa zai aura? Wasu suna ganin, zaka kalli iya kanta zuwa wuyanta da tafukan hannuwanta, Sabida nan ba al'aura bane, Wannan itace fatawar Sheik Nasiruddeenul albani. Wasu malaman suna ganin zaka kalleta da irin shigar da take zuwa wajen mahaifinta, wato ba tare da shijabi ba. Wasu kuma sukace, zaka kalleta a yanayinsu na zamankewarsu ta gida, Sabida an sami wani daga cikin magabata na kwarai da yake son auren wata yarinya yakenje yana kallon ta daga zanar gidansu ba tare da ta sani ba, sukace Annan ne zakaga kyawunta na asali. Amma yanzu mata suna ciko da shafe-shafe da goge-goge da sauransu, bazaka gane kyawunta na asali ba. Haka wasu malaman kuma sukace zaka ganta tsirara ne koda akwai wani abu dake boye a tattare da ita. Amma dai wannan fatawar Malamai sunyi watsi da ita, Sabida bai kamata ganin tsiraicin wani ba. Magana ta karshe dai, shi aure ana son Kayiwa mace kallo irin wanda zaija hankalinka ya zuwa gareta, wato ya zama dai ka ganta kafin ya aureta, kar daga baya kaga wani abu a tattare da ita kazo ka Dora mata karan tsana. Sabida wani sahabi ya auri wata mata a madina, sai yazo yace da manzon Allah saw nayi aure, sai manzon Allah saw yace dashi, ka ganta? Yace ban ganta ba ya manzon Allah!!, sai manzon Allah saw yace dashi, koma ka ganta Sabida matan madina suna da tsawarya a idanunsu. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)