TAMBAYA TA 3,171

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,171:*
=
Ina so ayi min Karin bayani game da suratul MUNTAHAN aya ta goma 10.
=
=
Amsa
=
_Toh wannan sedai mubaka takaice kwarai, domin idan akace bayani zamuyi sosai gameda wannan ayar to muna iya fin wata guda bamu gamaba, amma dai atakaice abinda ayar take cewa shine *YAKU WADANDA SUKAYI IMANI IDAN MATA MUMINAI SUKAZO MUKU SUNA MASU HIJIRA TO KU JARABASU, ALLAH SHINE MAFI SANI GA IMANINSU. TO IDAN KUNSAN SU MUMINAINE KADA KU MAYAR DASU GA KAFIRAI, SU MATAN BASU HALATTA GA AURENSU, SUMA KAFIRAN BASU HALATTA GA AUREN MATAN, KU BASU ABINDA SUKA BATAR NA DUKIYA KUMA BABU LAIFI AKANKU GA KU AURESU IDAN KUN BASU SADAKOKINSU KUMA KADA KU RIKE AUREN MATA KAFIRAI KUMA KU TAMBAYI ABINDA KUKA BATAR NA DUKIYA WANNAN HUKUNCIN ALLAH NE YANA HUKUNCI TSAKANINKU KUMA ALLAH MASANINE MAI HIKIMA******_
       _Wannan shine fassarar ayar a takaice. Sedai kuma ruwayoyi sunzo dadama gameda sababin saukarda ita. Misali akwai qissarda Wahidi yakawo acikin Asbabun Nuzul cewa: sadda aka umarci muminai  dasu dena jibintar mushirikai se akai hukunci da wannan gameda muminai akan yin hijira daga garin kafirci zuwa garin musulinci, wanda kuma aure shine babban abinda yake sanya soyayya tsakanin mushirikai da musulmi. To se wannan ayar tazo tana bayyana matsayin muhajirai mata. To bayan anyi sulhun hudaibiyya tsakanin Annabi da mushirikan makka cewa duk wani dan garin makka idan yazo wajen Annabi to ze mayar musu dashi, kwatsam sega wata mata me suna Su'aida kokuma Subai'ah bintul Harith Al'aslamiyya tazo bayan an kammala rubuta wannan sulhun ga Annabi nan kuma bebar hudaibiyya ba, saiga mijinta wanda shi kuma kafirine kawai yazo wajen Annabi a sukwane sunanshi Sayifi binu Rahib yace Ya Muhammadu dawomin da matata domin kaine kayi sharadin haka gama littafine tawadar ko bushewa batayiba. Nan take se Allah ya saukarda wannan ayar****_
      _Wasu kuma sukace Ummu Kulthum bintu Uqubah binu Abi Mu'ad ce tazo, saiga danginta sunzo sune neman Annabi ya mayarmusu da ita, akace ta gudone daga wajen mijinta Amru dan Ass tareda 'yan uwanta Ammar da Walid, sai Annabi (s.a.w) ya mayarda 'yan uwan amma ita be basu itaba, sai sukace kadawo mana da ita akan sharadinda mukayi, sai Annabi yace ai sharadin namu akan maza ne be shafi mata ba, se Allah ya saukarda wannan ayar, wannan kissar tana cikin Bukhari (2734). Wannan ayar dai ta samu Sabubban sauka dayawa, wasuma sukace ta saukane dalilin Umaimah bintu Bashar matar Thabit binu Shimrakh seta gudu daga wajenshi dominshi kafirine a lokacin seta koma madina ta auri Sahalu binu Hanif har ta haifa masa Abdulkahi. Wasu kuma sukace ta saukane don tayi qaidi ga wancan sharadin cewa mazane kawai idan sukazo wajen Annabi ze mayar dasu banda mata. Sekuma ayar tana kara tabbatarda haramcin mace musulma ta auri kafiri, sannan kuma tana halastawa maza musulmai su auri mace musulma wacce tayo hijira tabaro mijinta kafiri acan kasar arna amma dai abata sadakinta. Bawai kawai zaka riketane tazama matarka babu sadakiba. Wannan shine a takaice domin nan ba filin tafsiri bane baze yiwu mu bude bayanan dukaba. Allahu Ta'ala A'alam*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Post a Comment (0)