TAMBAYA TA 3,172

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,172:*
=
Naji wani malami yace game da musabaka ko wani abu makamancin haka, inde masu musabakanne zasusa wannan ya kawo nashi wannanma yakawo nashi ahada duk wanda yaci wannan gasar abashi to haramunne. Amma in wanine agefe wanda babu shi acikin gasar yasa kudin to babu laifi, to ya matsayin kacici da akeyi wanda mutanan da zasuyi kacicin susa kudi ko wani abu makamancin haka, duk wanda yaci adauka daga cikin abunda akasa abashi?
=
=
Amsa
=
_Toh wannan abinda malamin yafada ai qa'idace yabaka gamamma sedai kawai kaci gaba da qiyasi basekaje kanata tambaye tambayeba. Kawai duk abinda yazama hadawa zamuyi kai kakawo ni inkawo amma kuma karshe dayane zaici riba dayan ze dauki asara wannan shine ake cema caca wanda caca kuma haramunce, shine itama musabakar yadda yafada ai hakane, idan yazama taurarin musabakar kowa seda yabada wani abu amma karshe wani ya cinye sauran sukayi asara basuciba to tazama caca kenan, hakananma kacicinda kake fade inhar kawowa zamuyi sekuma dayanmu ya cinye to wannan shima haramunne domin cacane. Amma idan wanine yadauki nauyin gasar da aljihunsa to anan kuma kunga duk ma wanda yacinye bakuyi asara ba to wannan babu laifi. Hakama idan wasune can agefe suka dauki nauyin kacici kacicin bawai Aa iyakar su yan kacici kacicinne su akace kowa ga abinda zekawo sekuma mutum daya yazam yacinye sauran sunyi asara wannan haramunne. Kenan kawai abinda ake dubawa shine ace ansamu wanda zeci riba da wanda zeyi asara bayan kuma dukansu sunbada kudinsu wannan shine haramun****_
     _Allah ya tsaremu_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Post a Comment (0)