YANA SOYAYYA DA MATAR AURE
*TAMBAYA*❓
Assalamu 'alaikum.
Da fatan Mallam ya tashi lafiya. Allah Ya kara maka juriya kan aikin da kake na fadakar damu ,
aaameeen.
Mallam tambaya ce nike so dan Allah ka amsa mani.
Nine mukayi soyayya tare da wata har ta kaimu ga shirin yin AURE, to sai Allah cikin ikonSa Ya kawo wani dalilin da auren bai yiwu ba. Ni na auri wata
ita kuma ta auri wani. To amma sai ya kasance har yanzu muna waya, ta kan kirani nima nakan kirata wasu lokutan,kai har ma takai ta taba zuwa gidana
sun gaisa da matata.
Sai dai duk wannan wayar da muke da ita ba soyayya muke ba, babu kuma sauran soyayya
tsakaninmu, kuma har ila yau, DA IZININ MIJINTA MUKEYI, YASAN MUNA GAISAWA.
To Mallam yaya hukuncin wannan gaisawar da muke
da ita? Ka huta Lafiya
DAGA :- MUSA SALISU ALIYU
KADUNA
AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Shi Ubangijin da ya halicci Maza da Mata, yasan irin maganadisun da ya sanya acikin Jikkunansu ta fuskar sha'awa da son Mu'amala da junansu. Shi yasa ya Umurcesu dasu nisanta da Junansu. Sai dai idan akwai alakar aure ko Haifayya ko shayarwa
atsakani.
Ita mace, dukkan Jikinta al'aura ne in banda fuskarta da tafin hannayenta. Muryarta ma al'aura ce. Shi yasa Allah ya haramta ma mace yin magana
da duk wani Namiji wanda ba Mijinta ko Muharraminta ba, sai dai idan akwai larura.
Kuma koda larurar tasa zatayi maganar, to an haramta mata yin rangwada Ko Kissah acikin
zancenta.
Wannan wayar da kukeyi da wannan Matar bai dace ba, kuma bai halatta ba. Musamman idan an dubi cewar alaqar soyayya irin ta neman aure ta taɓa shiga tsakaninku.
Kasancewar wai Mijinta ma ya sani amma bai hanata ba, wannan ba ya nuna halarcin yin hakan.. Sai dai hakan yana nuna cewar shi Mijin nata
watakila ba ya kishin matarsa ne. Wato shi DAYOOTH NE.
Manzon Allah (saww) yace "DAYYOOTH BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA" (DAYYOOTH SHINE MUTUMIN DA YAKE TABBATAR DA BARNA ACIKIN LAMARIN IYALINSA, AMMA BA ZAI DAUKI MATAKI BA).
Idan kace ai ba Soyayya kukeyi ba, to shin QIYAYYA KUKEYI?? Kuma shin menene dalilin Qulla wannan Zumuncin atsakaninku??
Gaskiya ya kamata ka nisanceta. Domin kuwa shaitan zai iya Sanya Fitina atsakaninku. Ko ta bangarenka ko nata. Don haka ya wajabta ka nisanceta kasancewarta Matar wani.
Allah ya sawwake.
08031319129
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177