TAMBAYA TA 3,178

*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,178:*
=
Gameda tambaya ta 3,170  wasu mazan zakaga basuda komai matan keyi amma duk dahaka baya godewa kuma bayagani to wannan inmutum yayi adole bayadda ya iya tunda yayansa Allah bazai bashi lada ba ?
=
=
Amsa
=
_Kwarai kuwa babu ladar da za'a bata, domin dawainiyar 'ya'yan ba itace aka dauramaba, da ita da 'ya'yan wajibine akan mijin ya kula dasu inkuma ya gaza to tana iya neman saki kokuma ta makashi kotu acan za,a hukuntashi kuma alkali zesashi dole yakula dasu, inyaqi se kotu taraba auren. Amma idan itace da rajin kanta ba turasasata akayiba kawai itace domin kyautatawa da neman lada se take daukar nauyin kanta dana 'ya'yanta to wannan itace take samun lada, amma duk wanda yakeyin abu dan dole ba dan Allah ba to wannan wahalar banzane. Kamata yayi inzatayi to tayi saboda Allah dakuma kauna da tausayin mijin amma bawai ace dan doleba kokuma ace wai babu yadda zatayi wannan kuma karyane******_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Post a Comment (0)