TA CIRE SON ZUCIYA DA ƘISHI TA ZAUNA A GIDAN MIJIN TA SHINE YAFI ALKHAIRI GARE TA

TA CIRE SON ZUCIYA DA ƘISHI TA ZAUNA A GIDAN MIJIN TA SHINE YAFI ALKHAIRI GARE TA


:
https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Mallam kawatace take Neman shawara tasamu matsala da mijinta akan tasameshi da charting wata kuma soyayya sukeyi su biyu ne awajen mijinta kuma shi matafiyi ne Mallam Yana wata uku kamin yasamu zamada iyalansa amma kuma ya na da ra'ayin kara aure, sai tazo tagane Yana charting da su abind yana damunta sosai Mallam ita kuma tace idan ya yar da yakara aure za su rabu INA son kubata shawara Mallam zai mata sauki
:
*AMSA*👇
:
Wa Alaikis Salaam:- toh Shawarar da zan bata Gaskiya tayi Hakuri ta zauna a Gidan Mijin ta Musamman ma idan Akwai Yara a Tsakanin su. Ta Cire duk wani Ƙishin ta ko ganin rashin Dawowa ko Adalcin da Baya yi Musu ta bar shi yayi Auren sa ita ta zauna Gidan ta shine Yafi Dacewa.

Dalilai sune Kamar Haka:- Shin idan ta rabu dashi ina ne zata je? Shin wani Namiji ne a Wannan Lokacin zai Aure ta Sannan ya zo yana kula da ita da Yaran ta? Shin idan sun rabu tana da Tabbacin Cewa tana gama idda zata samu wani Namiji da zai Aure ta a Lokacin da take ne? Shin idan ta samu Mijin da Zai Aure ta, ta San yaya Halin sa yake ne? Ko halin sa yafi na Wannan Mijin da take tare dashi ta sani ne? Shin idan sun rabu wani ya aure ta shi wannan zai iya kula da ita ne da yaran ta yake sauke Hakkin sa Kamar Yadda wannan baya dawowa har wata uku ko biyu? Shin idan sun rabu har yaushe ne zata zauna kafin ta sake samun wani Namijin ta Aura? Shin Iyayen ta ba za su kulla mata bane da ita da yaran ta? Da ita ne mai bada Abinci abun sha ga wanda ta ga damar ba shi, idan sun rabu fah? Rashin Lafiya sutura komai a ina ne zata samu Kuɗin yi ko da kuwa a Yanzu ita ne mai yi da Kanta, idan sun rabu yaya zata yi ta samu? idan ma tanada halin siya shin tana ganin ba zai kare bane? Shin tana gidan Mijin ta Kullum tana samun Lada duk da Saɓanin da suke samu, toh yanzu idan sun rabu kuma ta gagara yin Auren a ina zata Samu ladan Auren? 

 Sannan tanada Sha'awa Kullum zata so Namiji yayi Jima'i da ita duk da dai ta saɓa da Wannan mijin da baya dawowa, toh amma yaya zata yi idan sun rabu bata yi Auren ba kuma tana bukatar Namiji? Shin wani hali ne Yaran ta za su shiga idan sun Rabu? Ko kuma ita wani hali ne zata tsinti Rayuwar ta a Cikin sa idan sun Rabu dashi? Waye ta san zai neme ta? Hannun waye zata faɗa? Gara wannan Mijin da suke tare ta san Halayyen sa wata kila gaba da baya, kuma har ta iya zama da shi na Shekaru, toh idan ta Rabu da shi, Hannun waye ta faɗa? Wata kila tayi Rashin Sa'a ta samu Halin miji na Biyun ya Nimka na wanda suke tare yanzu a rashin Ƙyan hali da rashin dawowa da wuri, kenan sai ta sake Cewa wannan ma ya sake ta ne? Wata kila ita Karamar Yarinya ce, tana ƴar Karama tayi Aure Biyu yanzu tana neman na Uku? Ya zata yi da yaran da take ta Haihuwar su tana Rarraba Ubannin su?

Kadan daga Cikin Dalilai, saboda haka ina bata Shawarar da ta Cire duk wani Kishi da son Zuciya ta zauna a Gidan Mijin ta Lafiya-lafiya tayi masa Ladabi da Biyayya in ba shine yace ya sake ta ba, toh ta bar shi yayi duk Abunda zai ko Mata 3 zai Karo yayi, ai yadda take fama da wahala haka suma matan zasu zo suyi fama duk Wanda bata da hakuri irin nata da Juriya sai ta rabu da shi, nan ne shi kuma zai gane Cewa Lallai ita wannan ne mai son sa. Don Haka ta bar shi yayi Auren sa babu Ruwan ta dashi ta ma cire komai nata daga kansa na batun Auren sa, kawai tayi masa fatan Alkhairi idan ya nemi Shaawar ta ta ba shi Shawara mai ƙyau sannan ta zauna dashi Lafiya ayi Auren. Idan kuma tace zata ɗaga Hankalin ta, ta ce su Rabu sai su rabun kuma yayi Auren sa a bar ta da Ciwon Zuciya da hawan Jini su zo suna more Rayuwar su itama kuma tayi fama da Jinya, shin ta yi gaba ne ko tayi baya? Sabida Haka babu Ruwan ta da Chartting ɗin da yake yi da wata idan na ɗiban Zunubi ne Zunubin ai Kansa zai Je bawai Kanta, abu ɗaya ne shine idan Misalin Yana aikata Zina a Waje da Matan Banza, toh nan ne Domin Kare kanta daga Kamuwa Da Ciwo Sai ta je tayi Gwaji bayan tayi Gwaji idan babu Komai Shikenan, domin gudun kamuwa da Ciwo Zata iya Cewa ya Sake ta Saboda Neman Matan Banza da yake yi, amma idan Kawai Charting yake yi Kuma Aure zai yi babu Ruwan ta. Don haka wallahi ta zauna a Gidan Mijin ta yafi, ta bar sa yayi Auren sa ta zuba masa ido ta ga gudun Ruwan su yayi Auren, sannan ita ta lura da irin Abunda mijin yake so da Abunda baya so ta gyara Rayuwar Auren ta yadda zata faran ta mata rai. 

Ko da an yi Auren Kada Kishi ya hana ta yi masa Biyayya da Bin Umarnin sa, komai ta rika yin sa abisa Koyarwan Addinin Musulunci ba tare da ta Ketare ba, Matukar tayi haka zatayi nasara a Rayuwar ta. Dafatan ta gane koh? 

 Wallahu A'alamu

 MUHAMMAD TUKUR JALINGO

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

2 Comments

Post a Comment