TAMBAYA TA 43

TAMBAYA ======== 👇 Slm,,tambayana shine zan iya yin wankan tsarki ba tare da najika gashin kaina sharkab ba? Tambaya na 2 shine da wane lokacine mutum zaiyi niyyan wankan tsarki,,yana shiga bandakin ne ko kuwa AMSA ====== 👇 Dole ne idan kikazo wanka sai kin jika gashin kanki sharkab da ruwa, sai inda wata larura ne anan kuma anyi miki uzurin zakike yin taimama, idan kika warke sai kiyi wanka din kuma, amma dai da wannan ne ruwan zai sami damar shiga ko'ina a jikinki. Na biyu kuma, daga lokacin da zakiyi wanka tin kafin ki kai ruwa bandaki kin kaddara cewar zakiyi wankan tsarki, Sabida haka babu wani bukatar sai kin furta abinda zakiyi, Allah ya fiki sanin abinda zakiyi, kina sanar dashi ma wani bata lokaci ne. Kuma idan kika furta da bakinki anan ma kinyi bidi'a. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)