TAMBAYA TA 2,802

*Asssalamu Alaikum* . . *Tambaya ta 2,802:* = Mune mukeyin aikin gidan biredi to sai sallar juma a takama kuma munsa biredi acikin tanda idan mukatafi sallah biredin zai kone to yaya zamuyi, kuma cikin mu bamai yarda wasu sutafi wasu sutsaya = = Amsa = = _Toh Qa'ida ta Addini shine DAR'UL MAFSADA MUQADDAMUN ALA JALBUL MASLAHA wato akan gabatarda tunkude 6arna akan a janyo amfani, zuwa kuyi sallar jumu'u acikin jam'i wannan babu shakka amfani ne, amma kuma barin wannan biredin ya lalace shikuma 6arna ce, to yanzu anan asali abinda yafi kamata kuyi shine asamu wasu mutum daya ko biyu su zauna sulurar muku da wannan biredin sauran kuma suje suyi sallah. In kukayi haka to wadannan da suka hakura suka zauna qarshenta in Allah yaso yana iya basu kadarda tafi taku ku wadanda kukaje kukayi sallar gwargwadon irin niyyarsu saboda wadannan da suka tsaya tamkar Ribadi ne sukayi na kulawa da dukiyar musulmai, sannan kuma idan basu tsayaba to ku kanku bazakuje wannan sallarba bare har ku samu ladan da kuka samu. Inkuma wannan bata yiwuba kowa yaqi yarda ya tsaya to sai kuyi quri'a duk wadanda tafada kansu sai su tsaya sauran kuma suje suyi sallah sudawo. In ita wannan din bata yiwuba shikenan sai ku hakura da zuwa sallar dukanku seku hadu kuyi jam'in sallar azahar****_ _Amma daga wannan ranar sai kudena gangancin daura fulawar taku a daidai lokacin sallah ku dinga bari sai kundawo sallah kokuma kuzo kuyi dawuri kafin lokacin sallah*****_ _Inhar dagangar ne kuke qin daura abin naku sai kunbari lokacin sallah ya kusa kuke daurawa Toh wannan baya halasta kuqi zuwa sallar jumu'a domin wajibine kuma babu larura akanku sedai kubar abun naku kusan nayi*****_ = = Allah Yasa mudace . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . *مجلس تعليم الكتاب والسنة* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ . ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. . Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
Post a Comment (0)