TAMBAYA TA 50

TAMBAYA ========= 👇 Tambayata ta farko ni ma'abucin sauraren wa'azine akowane wuri kuma akowane lokaci hattama acikin toilet na kan iya kunna wa'zi a wayata ina saurare ina wanka ko wata lalura. Tau malam ko hakan ya halatta? AMSA ===== 👇 Bai halatta ka shiga bandaki da wani abun da yake dauke da sunan Allah ba, ko kuma ka kunna radio ko waya alhalin ana karanta Alqur'ani kai kuma kana bayan gida, Wannan Haramun ne. Sai dai idan kana bukatar kar karatun da akeyi a radio idan wata tasha ce ka kamo Dan kar Wannna program din ya barka, zaka iya kawo radio din ka ajiye daga waje kana sauraron abinda akeyi,. Ya tabbata daga cikin magabata suna sanya yayansu suna karanta musu littafin ilimi ko Alqur'ani suna sauraro alhalin Su kuma suna bandaki, Sabida kwadaituwa da wannan ilimin, Dan kar suyi hasarar wannan Lokacin ba tare da sun saurari wani abinda za'a rubuta musu lada ba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)