DUK YARAN DA MUKE HAIFA DA MIJINA SIKILA NE, ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI NA AURI WANI?

*_DUK YARAN DA MU KE HAIFA DA MIJINA SIKILA NE, ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI NA AURI WANI_* *Tambaya* Assalamu alaikum dafatan anwuni lafiya malam, dan Allah malam ina neman shawara ina da aure 'ya'yana ukku, na farko yana da 7yrs kuma yana da sikila na biyun yana da 5yrs sai ta ukkun nada 2yrs itama tanada sikila watanta biyar yanzu da rasuwa, sai dayan Wanda baida sikilar ya fara ceman kafarshi na ciwo ba ayi awaba kuma hannunwanshi suma suka fara ciwo, sai duka jikin shima ya dauki ciwo, shima mai sikilar sai ya.fara ciwan,.muna zuwa asibiti aka basu gado muka kwanta sun tambaye mu Wanda bai da sikilar mun yi mashi awo.ne mukace aa, saboda tunda akai haifeshi bai taba ciwo ba sai mura da dan zazzabi shima na rana dayane yawarke to sunyi mana bayanin cewa wata sikilar nadadewa kafin ta bayyana to sai ya rasu, shima dayan kwana daya da rasuwar wancen sai ya rasu kuma kanwarsu wata biyar tsakaninsu hankalina ya tashi yanzu banda 'ya'ya kuma ni kadaice wajen mijina, shi ya kuma fadi mani dole yakara aure ni kuma ya ce sai nan da shekara goma yake san in haihu ni.kuma inasan 'ya'ya kuma ina san mijina amma ban san in haihu da shi saboda na sha wahalar yara kuma jinin mune daya kaga dole tinani ya dame ni, shin zan iya cewa mijina ya sauwake mani inje insamu wani Wanda zan iya haihuwa yara ba sikila ba?? dan ALLAH inasan Karin bayani nagode *Amsa* Wa alaikum assalam, Tabbas Kina cikin damuwa da tashin hankali, Tun da kin zama Mai wabi. Allah ya shar'anta saki ne Domin tunkude cuta daga daya daga cikin ma'aurata Ko dukansu Kamar yadda ayar Suratun Nisa'i ta tabbatar da hakan. Mutukar kin ga a cigaban zamanku akwai cutarwa kina iya neman rabuwa da shi Ko ta hanyar saki Ko fansar kai. Yana daga cikin manufofin aure samun zuriyya wadanda za su debe kewa. Idan Kuka rabu Allah zai iya azurta kowa daga falalarsa, ya ba ki miji ya kuma ba shi matar da in sun hadu ba za su haifi Sikila ba. Allah ne mafi sani 22/04/2018 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)