MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA

*_MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA!_* *Tambaya:* Assalamu alaikum malam Ina son karin bayani game da manufofin sharia akan haramta zina. *Amsa:* Wa'alaikum assalam, Addinin musulunci ya zo don ya kare tsatson Dan'adam da mutuncinsa, don haka ya shar'anta aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin da haramta zina ya kunsa: *1.* Katange mutane daga keta alfarmar shari'a. *2.* Samar da Dan'adam ta hanya mai kyau, ta yadda za'a samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi ta hanyar zina, to ba za'a samu wanda zai kula da shi ba yadda ya kamata. *3.* Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna. *4.* Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja. *5.* Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a bayyane. *6.* Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa, sai fitintinu, su yawaita. *7.* Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane. *8.* Kare mutuncin yaron da za'a Haifa, domin duk yaron da aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci. *_WANNAN YA SA BABU WANI ZUNUBI BAYAN SHIRKA DA YA FI ZINA._* Allah ne mafi sani 21/4/2013 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)