NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU KO ZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH?

*_NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KO ZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH?_*

                                 *Tambaya:*
Aslm inada Tambaya Malam, Shin idan an fara sallah ka zo za  ka bi, za ka karanta addu'ar da ake yi ne bayan kabbarar harama? 

                                     *Amsa*
To dan'uwa abin da malamai suka fada shi ne: mutukar ya riski liman a mike, to zai yi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, ko da kuwa a raka'a ta biyu ne, saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare da shi, kuma addu'ar bude sallah za ta fadi daga kansa, saboda wurin yinta ya wuce.

Raka'ar da ka fara samu tare da liman, ita ce raka'ar farko a wajenka, wannan ya sa za ka yi addu'ar bude sallah, ko da kuwa shi liman a raka'a ta uku yake ko ta hudu, wannan shi ne zance mafi inganci.

Idan ka riski liman a tsaye amma abin da ya rage ya yi ruku'u, ba zai isa ka karanta addu'ar bude sallah ba, sannan ka karanta Fatiha, to za ka karanta fatiha, ka bar karanta addu'ar bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunna ce, karanta fatiha ga mamu wajibi ce a wajan wasu malaman.

Don neman Karin bayani  duba Al-majmu'u na Nawawy 3/276 da kuma Majmu'ul fataawa 30/150.

Allah ne mafi sani.

11\4\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)