*PAGE:*Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia
.
INA CIKIN SALLAH, SAI NA TUNA AKWAI NAJASA A HULATA?
_____________________
TAMBAYA:
_____________
Aslm Mallam,mutun ne yana tsakiyar sallah ya kai raka'a ta biyu sai ya tuna kamar akwai najasa a hularsa,amma bai tabbatar ba sai ya cire hular, ya cigaba da sallah,toh ya sallar sa take?
.
AMSA:
________
Wa alaikumus salaam, wanda ya tuna da najasa a hularsa, zai iya hanzari ya cire ta ya yar, in har ya yi haka sallarsa ta yi, saboda abin da aka rawaito cewa:
.
Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, wani lokaci yana sallah, sai ya cire takalminsa, daga baya sai yake bawa sahabbansa labari cewa:
.
Jibrilu ne ya ce maşa akwai najasa a jiki, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Nawqawy ya inganta shi a Al-muhazzab 3\132, hadisin sai ya nuna ingancin sallar wanda ya yı haka, tun da ba'a rawaito Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, ya sako sallarsa daga farko ba.
.
Allah ne mafi sani.
________________________________
AMSAWA: Dr. Jamilu Zarewa
RUBUTAWA: Abdulrazak Ahmad Jibia
WHATSAPP:
07015426669
08102933059
07037962390
08167498472
08065899940
08068902943
08065562163
09020100708
07068681111
EMAIL:
www.sheikhibrahimsabi'ujibia@gmail.com