INA DA SHEKARU 28,WACCE MACE YA KAMATA NA AURA?

*_INA DA SHEKARU (28), WACCE MACE YA KAMATA NA AURA?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum, dafatan Malam yana cikin qoshin lfy Allah sa haka amin. Malam inaneman shawara, Wace mace yakamata na aura amatsayina na dan shekara ashirin da takwas 28-29. yar shekara nawa tafi dacewa dani ayanzu?. Allah sa mudace amin. *Amsa:* Wa'alaikum assalam, ka auri mai addini, wacce Idan ka kalleta za ta burge ka, mai sonka, mai nutsuwa da sanin ya kamata, yana da kyau ka Sami matar da ka fi ta kudi da ilimi, ta fi sonka, ta kuma fika kananan shekaru, Ka tsaya ka kalleta da kyau, kafın ka aure ta, kada ka yi gaggawa. Allah ne mafi sani 16/03/2016 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)