*Asssalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,236:*
=
Naji wani karatu malamin yanacewa nana Aisha da annabi ma sun haura (sunyi fada) dan Allah inason jin gaskiyar tarihin?
=
=
Amsa
=
_Badai fada ba, sedai ace sun sami sa6ani, wannan kuma kakaf matan Annabi idan kacire Khadija to zeyi wuya idan akwai wata wacce basu ta6a samun sa6aniba, kamar irinsu hafsah ita har sakintama yayi akace ya maida ita. Kuma samun sa6ani tsakanin Annabi da matarsa wannan naya nuna cewa bata sonshi domin wannan yana babin mu'amalane, kuma Annabin shi dakansa yace su mata karkatattune idan kace zaka mikar dasu sedai kasakesu, dan haka wannan karkatan kakaf matan duniya idan kacire Khadija da Asiya da Maryam da Fateema, to babu wata mace wacce ba a karkace takeba sedai ka zauna da ita da hakuri kawai to suma matan Annabin dukansu sunada wannan karkatan shiyasa yadan sassami matsala dasu har yataba yin musu kaura yakoma masallaci, dan haka bawani abin zargi bane dan Annabi yasamu wannan matsalar, sannan kuma kai matarka idanda ace batada wannan karkatan to ko zaman kwanaki uku bazakuyiba zaka kadata gidansu, dan haka wannan karkatan shima yanada amfaninshi domin kuwa Allah baya aikin banza wanda bashida fa'ida*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika