INA HUKUNCIN AIKI DA BANKUNAN DA SUKE DA KUDIN RUWA?

*_INA HUKUNCIN AIKIN A BANKUNAN DA SUKE DA KUDIN RUWA?_* *Tambaya:* Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu. Malam tambayata Itace shin ya hukuncin aikin banki ga musulmi? Da gaskene haramun ne? Don Allah a wayar mana dakai. Bissalam *Amsa* To dan'uwa Annabi ï·º yana cewa: "Allah ya la'anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1598. Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike.. Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401. Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka. Allah ne mafi sani. 20/03/2016 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)