SITTU SHAWWAL



SITTU SHAWWAL

Rubutun Dr Kabir Abubakar Asgar 

- Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “wanda yai azumin watan Ramadan sannan ya biyo bayan sa da azumi guda shida a watan Shawwal to za a ba shi ladan azumin shekara”.

- Wannan hadisi shine madogara game da mustabbancin yin azumi guda shida a watan Shawwal.

- Ya halasta a fara azumin daga biyu ga watan Shawwal.
- Ana iya yin azumin a jere ko a yi su a rarrabe gwargwadon hali. 

- Abin da ya fi dacewa da wanda ake bi bashin azumin wasu kwanakin Ramadan shine ya fara da biyan bashin da ake bin sa.

- Ba shi daga cikin sunna yin wani biki ko murna ta musamman a washe garin gama Sittu Shawwal.

- Matar aure ba ta yin azumin nafila matukar maigidanta na gari sai da izininsa.

- Allah ya sa mu dace.
Post a Comment (0)