MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?

*MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?* *Tambaya* Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka. Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid? *Amsa* Wa alaikum assalam, Bai halatta ga mai takaba ba ta fita zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031) inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki kammala iddarki" Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba za ta fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a sharia. Imamu Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi bayani cewa "Dukkan Mata ana fitar da su daga gidanjansu Don su halarci idi, in ban da wacce take iddar mutuwa. Allah ne mafi Sani 03/09/2017 *Dr, Jamilu Zarewa*
Post a Comment (0)