SALLAR NAFILA LOKACIN DA LIMAN YA HAU MINBARI RANAR JUMA'A

Sallar nafila lokacin da liman ya hau minbari ranar Jumu'ah.

√  Sheikh.Jabir Sani MaiHula

1) Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu'ah liman yana akan minbari, zaiyi sallah raka'ah biyu, amma ya gajarta. (Bukhari da Muslim)
2) Idan mutum ya taradda ana kiran sallah kafin a fara khutbah, zaiyi sallah lokacin da ake kira bazai jira a gama kiran sallah ba, saboda sauraron khutbah wajibi ne amma sauraron maikiran sallah Sunna ne. ( Ibn Uthaimeen)
3) Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, bazaiyi sallah ba lokacin da liman ke khutbah, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci.
4) Mutane da yawa sukanyi kuskure sai su zata akwai wasu raka'ah biyu da akeyi kafin Jumu'ah, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana khutbah. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana khutbah.
5) Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka'ah biyu kafin ya zauna. Wannan hukuncin da ranar Jumu'ah da Assabar da sau ran ranaku duka daya ne. Dalili akan hakan shine, cewar da Manzon Allah S.A.W. yayi: Idan dayanku ya shiga masallaci kada ya zauna sai yayi sallah raka'a biyu. ( Bukhari da Muslim)
Ya kamata ayi fadakarwa da mutane akan wannan hukuncin, saboda da yawa akan saba.

Allah yasa mudace da sunnah. Don Allah ayi kokari a yada domin yan uwa su karu.

Post a Comment (0)