TAYI ALWALA DA RUWAN FITSARI HAR TAYI SALLAH BATA SANI BA

*_TAYI ALWALA DA RUWAN FITSARI, HAR TAYI SALLAH BA TA SANI BA_* *Tambaya* Assalamu alaikum. Nakasan ce lokacin da Ina bording school idan senior na ya aikeni debo ruwa kafin na kawo masa ruwan sai nayi fitsari acikin rowan, kuma ban san adadin mutanen dana yiwa hakan ba, saboda ganin yadda senior yin mu suke gallaza mana da sunan seniority ga shi yanzu ban san inda zan gansu ba ballantana na nemi afuwar su, me ya kamata na yi kenan a yanzun? nagode, Allah ya kara maka imani da ilmi mai amfani *Amsa* Wa'alaikumus salam, To 'yar'uwa ina rokon Allah ya kare mu daga irin wannan danyan aikin, Allah ya sa su kuma shawagabannin makarantu su kula da irin wannan cin zalin, ina baki shawara ki yawaita istigfari, mutukar lokacin da kika yi hakan kin balaga, su kam sallarsu da wankansu sun inganta, saboda a zance mafi inganci na malamai duk wanda ya yi alwala da ruwa mai najasa, bai kuma gano hakan ba, sai bayan lokacin sallar ya fita, to ba zai sake sallar ba, haka ma wanda ya yi wankan janaba, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki. Duba Al'ausad na Ibnul- munzir shafi na 18. Allah ne mafi sani. 14\2\2015 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)