ZAN IYA CI GABA DA ZAMAN AURE DA MASHAYIN GIYA?

*_ZAN IYA CIGABA DA ZAMAN AURE DA MASHAYIN GIYA??_* *Tambaya* Assalamu alaikum malam tambayata mijinane mutum Mari Shaye Shaye kuma Allah ya azurtamu da haihuwa Yara hudu Don Allah meye hukunci zamana dashi a addini shin babu laifi ko kuma akwai laifi? *Amsa* Wa'alaikum assalam, Ki yi kokari wajan yi masa nasiha Allah zai iya shiryar da shi. In har kina son shi za ki iya cigaba da zama da shi. Wanda yake shan giya fasiki ne, saboda yana aikata babban zunubi, saidai tun da bai kai kafurci ba ya halatta ki cigaba da zaman aure da shi mutukar kina kaunar shi. Allah madaukakin sarki ya shar'anta saki saboda tunkude cutarwa daga ma'aurata, mutukar ba za ki iya tsayawa da hakkokinsa ba, ya halatta ku rabu, tare da cewa duba makomar yaranku yana da muhimmanci. Allah ne mafi sani. 24/3/2018 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)