Sallar WALHA

SALLAR WALLAHA

Sallar Wallah:-
"Tana cikin sallolin nafila mafi falala wadda Manzon Allah ﷺ yayi a aikace kuma ya kwadaitar akanyinta,sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ da yake kiyayeta hatta a lokacin Bulaguro".

HUKUNCIN SALLAR WALLAH
Sallar Wallaha sunnace mai karfi wadda aka kwadaitar akan kowane musulmi ya raya wannan Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon Allah ﷺ da bin Umarnin da kuma dacewa da falala da lada mai yawa.

●بن باز رحمه الله:-
Yana cewa:-
"Sallar Wallah sunnace ta Manzon Allah s.a.w mai karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar da Sahabbansa akan aikita ta".

Allah yana cewa:
*{ وَالضُّحَى}[الضحى:1]*
*Allah yana rantsuwa da Hantsi ko wallaha idan Allah yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna girmama wannan abu da matsayinsa awajan Allah".

DAGA CIKIN FALALAR SALLAR WALHA
Hadisan Manzon Allah ﷺ masu yawa sunzo masu bayyana falalar sallar wallaha, ga kadan daga cikinsu;-

1-Yazo acikin Hadisil Qudsy,Allah mai girma da Buwaya yana cewa:-
*{Dan Adam,kayi min Raka'o'i guda hudu a farkon yini,zai isarmaka wannan yinin zuwa karshensa}*
@أخرجه الترمذي (475).

"Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi sallar Wallaha raka'a hudu a farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da taimakonsa na musamman".

الطيبي رحمه الله تعالى:
Yana cewa;
*An zan isar maka al'amuranta da shagulgulanka da baka kariya da kiyayeka daga abin ki bayan sallarka ta wallaha har zuwa karshen yini,......"*.
@تحفة الأحوذي :2/478

2-Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Jikin mutum akwai gabobi guda 360,kuma an dora masa yin sadaka akan kowace gaba)* sai Sahabbai suka ce masa:
"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon Allah ??" sai yace;
*(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci,ko dauke wani abin cutarwa daga akan hanya,idan kuma mutum bai sami damaba,to yayi sallah raka'a guda biyu na Wallaha ya isar masa)*
@الألباني رحمه الله ,صحيح الترغيب

3-Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Babu mai kiyaye Sallar wallaha sai bayin Sallah masu yawan komawa zuwa ga Allah,sallar wallaha sallace ta bayanin Allah masu yawan konawa zuwa ga Allah)*
@صححه الألباني رحمه الله.


*ADADIN RAKA'O'IN SALLAR WALLAHA*

Mafi karancin Sallar wallaha raka'a biyu,amma bata da adadi wajan yawanta ko nawa ka iyaye,amma wasu Malaman sun tafi akan mafi yawanta shine raka'a Takwas kamar yanda Manzon Allah ﷺ bai wuce raka'a takwas ba kamar yanda Hadisin Ummu hany R.A ta ruwaito.

*LOKACIN SALLAR WALLAHA*

Lokacin Sallar wallaha yana farawane daga fitowar rana ta dan daga kadan kamar bayan fitowar rana da minti 30 zuwa 45am har zuwa gab da zawalin rana daga tsakiya da yan mintina biyar.
@ابن عثيمين مجموع الفتاوى (14/ 306))

Wato kamar;
*"Daga karfe 7am zuwa 11:45am*.

*MAFI FALALAR LOKACIN SALLAR WALLAHA*.
mafi falala da alkhairin lokacin yin Sallar Wallaha,shine lokacin da rana ta fara zafi sosai,lokacin da mutane sukafi shagaltuwa da aiyukansu na yau da kullum,kai kuma sai ka shagaltu da gani da Ubangijinka,gab da zawalin rana.
@اللجنة الدائمة (6/148)

بن باز رحمه الله:-
Yana cewa;
*"Abinda yafi muhimmanci shine idan mutum yana da damar yinta a lokacin mafi falala to yayi amma idan baya da dama to yayita a farkon yininsa,amma yinta lokacin da rana tafara zafi sosai yafi"*.

*ZIKIRIN DA AKE KARANTAWA BAYAN SALLAR WALLAHA*

Daga Nana A'isha رضي الله عنها tace;Manzon Allah ﷺ yayi Sallar wallaha,sannan yace;
* ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ, ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ , ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ*
"ALLAHUMMAGH FIR LI,WA TUB ALAIYA,INNAKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM" har sai da ya fadi hakan sau 100.
@رواه البخاري رحمه الله في اﻷدب المفرد وصححه الألباني رحمه الله حديث رقم 619.

●ابن عثيمين رحمه الله
Yana cewa:
*"Sallar wallaha idan lokacinta ya wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci kayyadadde"*.

●ابن باز رحمه الله:
Yana cewa:
*"Sallatul Ishraki wato Sallar hantsi itace sallar wallaha afarkon lokacinta,kuma sunnace ta kowace rana"*.

*Al

lah ne mafi sani*


Allah ka bamu ikon kiyaye wannan sunnah mai girma amin.

1 Comments

Post a Comment