_*Tambaya:*_
Aslm ina da tambaya pls
Kaman yadda akafada a hadis ba'a azumi ranan jumma'a Sai Dai a watan Ramadan toh Kaman yadda ake awanan watan shawal Idan kanaye sai yafada ranan jumma'a zakaye koh zaka tsalake.
_*Amsa:*_
_Gaskiya, ba haka hadisin yake nufi ba, Hadisin da ke nuni a kan azumi ranar *Juma'a* ba yana nuna haramcinsa bane kamar yadda malamai suka yi bayani, amma dai Makaruhi ne yin azumin nafila a ranar Juma'a sai dai idan mutum ya azumci *Alhamis* ko kuma yana da niyyar yin azumin a ranar Asabar._
_An kar6o hadisi daga Abu Huraira (r.a) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *((Kada dayanku ya yi azumi a ranar Juma'a, sai dai idan zai azumci yinin da ya gabace shi, ko yinin da ke gaban shi))* Bukhary da Muslim._
_Wannan hadisin ke nuna ba laifi mutum ya yi azumin *Sittus Shawwal* koma kowani iri a ranar Juma'a idan har ya yi a ranar alhamis ko kuma yana da niyyar yi a ranar Asabar._
_Kuma a magana mafi inganci, babu laifi mutum ya yi azumi a ranar Juma'a idan har ranar ta shigo jerin azumin da yake yi. Misali, idan mutum ya taho da azumin shi na Sittus Shawwal sai Juma'a ta shigo ciki, to zai yi azumi a ranar. Haka ma wanda ke azumin kaffara, ko na bakance, ko azumin da ake yi a tsakiyar wata, ko kalan azumin Annabi Dawud (A.S), wannan duka babu laifi mutum ya hada da ranar Juma'a in shaa Allah._
_abin nufi dai shi ne, karhancin (wato hanin) ya takaitu ne a kan wanda ya kebance ranar Juma'a ita kadai don yin azumi ko tsayuwar dare a cikin ta._
_Wallahu a'lamu._
_Daga dalibinku_
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_
Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.