CIYAYYA

CIYAYYA
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Wabarakatuhu.
Masu iya magana dai na cewa :
‘Kowa Ya Tuna bara bai ji dadin bana
ba’, wannan magana haka take,
domin kuwa halin da mutane suke
ciki a wannan lokacin sai dai muce
Alhamulillah. Sai dai, ina da wata
Shawari da nake fatar ta zama sauki
ga ‘Yan Uwa na Musulmi da Hausawa
baki daya.
A Zamanin da, Iyaye da Kakannin mu
suna da wata Al’ada da ake kira da
“CIYAYYA”. Ita dai wannan Al’ada,
ana Yinta ne kusan kullum kamar
haka : Abokai ne guda biyu ko kuma
sama da haka (masu aure ko Samari)
zasu dinga taruwa a kofar gidan su
daya daga cikin su ko kuma a wani
wuri na Musamman bayan Sallar
Magariba ko Isha’i, kowa in zai zo,
zai zo ne da Kwanon abincin daren
sa na wannan ranar,wasu kuma yara
ma ake turawa sukai abincin har
Wajen zaman iyayen nasu. Yayinda
wadannan abokai suka taru, sukan
Gaggaisa da juna sannan a danyi
Barkwanci a Tsakanin Juna, daga
baya kuma sai kowa ya wanke hannu
a fara cin abinci, in an gama cin na
wannan sai a ci na wancan har a
gama, a wasu Lokutan ma basa iya
Cinye Abincin sai dai su baiwa
Almajirai, in kuma wani yazo wucewa
to Sai ya tsaya ya ci rabon sa.
Wannan Al’ada tana da Sunaye iri iri
da ake kiran ta da shi, kamar yadda
naji wasu suna kiran ta da ‘CI MU CI’,
to amma ni dai na fi sanin ta da
Ciyayya.
Wannan shi ne iya abinda zan iya
Tunawa dangane da wannan Al’ada,
Kasancewar na zo duniya a dai dai
lokacin da wannan Al’ada ta fara
rauni sosai, Musamman a tsakanin
mutanen Birni.
To shi ne nake tunani, me zai hana
mu dawo da wannan Al’ada ta Iyaye
da Kakannin mu? Me zai hana mu
Dabbaka ta kuma mu Karfafi
Al’ummar mu da yin ta? A tunani na,
idan har muka dawo da wannan
Al’adar, Abubuwan da zamu Amfana
da su suna da Yawa. Ga kadan daga
cikin su ;
* Mutane zasu samu damar koshi
Yadda Ya kamata.
* Za’a Samu Soyayya da Shakuwa
sosai a Tsakanin Al’umma.
* Fahimta zata dinga shiga tsakanin
mutane a Maimakon rashin Fahimta.
* Zumunci zai Gyaru.
Ina Fatar Allah Ya Tserar da mu daga
Wahalhalun Rayuwa ameen.
Ya Allah Ka Azurta mu da Kyakkyawar
Fahimta ameen.
©Haiman Khan Raees
@haimanraees
08185819176
Haimanraees@gmail.com
January 2017

Post a Comment (0)