_*Tambaya:*_
Aslm ya ikwani wa akwati fil islam.ina tambaya ne shin dole daga hanu a sallah,misali kaman wurin yin sujjada da tasuwa.ko kowa in anyi kabbaran tada sallah yayi.wslm Allah sa mu xama cikin yan tattun baye ta sana diyyan wannan wata ta Ramadan.
_*Amsa:*_
_Daga hannu a cikin sallah yayin kabbarar harama hakki ne a kan kowane musulmi yayin da ya zo yin Sallah. Haka ma sunnah ne daga hannu yayin yin ruku'i da sujada._
Ya zo a hadisin Ibn Umar (r.a) cewa, _Lallai Annabi (ﷺ) ya kasance ya na daga hannunsa kusa da kafadunsa yayin da zai bude (fara) sallah da lokacin da zai yi kabbara don yin ruku'i da lokacin da ya dago daga ruku'i._ Bukhary da Muslim.
_Tun da kuwa har ya kasance Manzon Allah (ﷺ) na daga hannu lokacin *kabbarar harama,* da *ruku'i* da *dagowa daga ruku'i* wannan ke nuna muma hakki ne a kan mu mu yi riko da wannan sunnah. Domin Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Ku yi sallah kamar yadda kuka ga Ina yin Sallah”*_
_Saboda haka 'yar uwa ana daga hannu a dukkan Wadannan wuraren uku da muka ambata._
_Wallahu a'lamu._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_