MATAR AURE DA TAYI ZINA DA AZUMI

_*Tambaya:*_

Meye hukuncin matar da tai zina da aurenta kuama acikin watanan mai girma malam

*Amsa*

_Zina❗Ko ba a wannan watan ba haramun ne ga namiji ko mace, matar aure, bazawara da budurwa, dukkansu haramun ne su aikata *zina.*_

_Hukuncin matar aure da ta yi zina a guraren da ake Shari'ah ta Musulunci shi ne; hukuncin kisa ta hanyar jefewa._
.
_Duk macen da ta yi zina alhalin tana da aure haƙiƙa ta ci amanar mijinta, kuma ta tonawa 'yaƴanta da danginta asiri, saboda duk wani mutum kirki zai ƙyamaci auren 'yaƴanta don gudun gori daga bakunan mutane. Kuma ga babban cin mutuncin da ta yi wa mijinta wanda tabbas sai Allah ya bi ma sa haƙƙinsa a ranar alƙiyamah matuƙar be yafe mata ba._
.
_Saboda haka se ta yawaita Istigfari wato neman gafarar Ubangiji da tuba zuwa gare Sa cikin nadama da ƙasƙantar da kai._
.
_Sannan ta nemi yafiya a wajen mijinta cikin salo ba tareda ya gane abin da ta aikata ba._
.
_Sannan kuma ta yawaita neman tsarin Allah daga Shaiɗan a duk lokacin da zuciyarta ta fara raya mata ta yi zina da wani. Domin Shaiɗan ne ya ke son tunzura ta zuwa ga halaka._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_

Post a Comment (0)