HAUSA TA RIGA TA ZAMA HARSHEN K'ASASHEN
DUNIYA.
`
(M) Abba Muhd Danhausa.
`
Bana jin wata al'umma zata samu cigaban a zo, a
gani, ba tare da ta yi rik'o da harshenta da kuma
al'adunta ba, kamar yadda Farfesa Muhammad
Hambali Jinju (1990) ya ce, "Ilmantar da matasa cikin
harshe bako, misali Faransanci ko Ingilishi, ya
kasance ɗaya daga cikin dalilan lalacewar al'adu da ci
bayan ilmi da zamowar 'yan k'asa bak'i a cikin
k'asarsu.
`
Kamata ya yi Afirkawa su gane makircin Turawa 'yan
mulkin mallaka, tsofaffi da sababbi, kuma su binciki
harsunansu na kansu da al'adunsu nagari, su ciyar da
su gaba ba tare da ɓata lokaci ba. Harshe, kowane iri
ne, yana iya ci gaba da hanzari muddin masu shi sun
tsaya, tsayin daka, sun bincike shi kuma sun kare shi.
Wajibi ne Afirkawa su ci gaba da kasancewa Afirkawa,
ba Turawa Bakar Fata ba.
`
Samuwar harshen k'asa wanda kuma shi ne harshen
mulki da koyarwa ita ce ma'aunin girma da darajar
k'asa a idanun k'asashen duniya.
`
Abin kunya ne mutanen k'asa ɗaya su kasa fahimtar
juna sai cikin Turanci kawai. Haka kuma babban abun
kunya ne shugabannin Najeriya da na Nijar su gaza
yin hira kuma su kasa yin mahawarori masu amfani
kan k'asashensu, cikin Hausa, musamman in su 'yan
Najeriya na Arewa ne. Har ila yau babban abin kunya
ne 'yan Nijar da 'yan Arewacin Najeriya, in sun sadu
da juna, su yi ta zuba Ingilishi da Faransanci wai su
"Masu ilimi" kuma "Manyan mutane" suna kiran juna
mutanen "Faransi" da na "Ingilishi". Allah wadan
naka ya lalace!
`
Wajibi ne jama'ar Jamhuriyar Nijar da Tarayyar
Najeriya su himmatu da gaske wajen ɗaga matsayin
Hausa zuwa matsayin harshen k'asa kuma na mulki
da koyarwa. Wajibi ne kuma mutanen Najeriya da na
Nijar masu basira da k'okari su haɗa kansu kuma su
shawo kan ɓatattun 'yan'uwa masu nuna son kai ko
kuwa barorin Turawa. Su yi watsi, har abada, da duk
abin da zai kawo wa Afirka bala'i.
`
Hausa ta riga ta zama harshen k'asashen duniya.
Babu makamanciyarta a Nijar da Najeriya."
`
Mu yi amfani da damarmu, kar mu yi sake dama ta yi
amfani da mu.