IN ZAKA SA TUFAFI KO KUMA IN ZAKA YI ALWALA

🔗_*بسم الله الرحمن الرحيم*_🔗

_*Darasinmu na yau, hadisin da ke da ala'ka da tufafi 01 of 06.*_
°
°
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce:{IN ZAKA SA TUFAFI KUMA IN ZAKA YI ALWALA, TOH KA FARA DA ('BANGAREN) DAMA.}*_
°
°
```[Sahihul Ja'mi-i;787, Al-Mishkaat;401]```
~~
~~
_Wannan ke nuna mana muhimmancin gabatar da dama akan hagu a duk sa'ilin da za'a gudanar da wani aiki na alkhairi, haka Annabi Muhammad(SallalLaahu alaihi wa sallam) ya kasance yana yi. Haka kuma ana gabatar da hagu akan dama akan dukkan wani aikin qazanta. Allaahu a'alam_
~~
~~

Post a Comment (0)