_*Tambaya:*_
Assalamu alaikum malam dan allah inaso abani shawara kikuma addu arda zanrikayi wlh inacikin damuwa saboda adaduk abinda nasa gaba inaganin nasara amma yanzu abinya canza kome nayi bana ganin cigaba koda acikin mutane kwarjinina yaragu shine nakeso ataimaka mini nagode.
_*Amsa:*_
_WA'alaikumussalamu Warahmatullah._
_'Yar uwa, da farko dai ina baki shawara da ki gyara tsakaninki da Ubangijinki (ﷻ), ki kasance mai bin umarninSa da barin abin da Ya yi hani. Sannan ki yi duba a karan kanki shin Menene ki ke aikatawa wanda Allah da ManzonSa suka yi hani akai? Shin Kina kiyaye hakkokin Allah da ke kan ki?_
_Na biyu ina maki wasici da ki ji tsoron Allah, hakika idan ki ka kasance mai *Taqwah,* to Allah zai yi maki jagoranci a al'amuranki duniya da Lahira. Idan har mutum yana neman mafita a kowane rikici ya shiga, to Allah ze bashi matukar ya yi taqawah. *Allah (ﷻ)* Ya ce:_
_*”.... وَمَن يَتَّقِ اللَّهَ يَجعَل لَّهُۥ مَخرَجًا“*_
_*“.... Kuma wanda ya ji tsoron Allah, (Allah) zai sanya mashi mafita.”* (At-talaq: 3)_
_Idan kina so Allah Ya kasance tare da ke, kuma duk halin da ki ka shiga Ya kawo maki dauki, to ki kasance mai taqawah . Allah (ﷻ) Ya ce:_
_*”إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوا وَّالَّذِينَ هُم مُّحسِنُونَ“*_
_*“Lallai Allah Ya na tare da masu Taqawah da wadanda suke kyautatawa.”* (An-Nahl: 128)_
_Saboda haka 'yar uwa ki ji tsoron Allah, ki kasance mai biyayya ga dokokinsa, tare da sadaukar da al'amuranki gare Shi, In shaa Allah za ki ga chanji a rayuwarki._
.
.
Sannan ki dinga yin wannan addu'ar:
_*ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺩِﻳﻨِﻲ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻫُﻮَ ﻋِﺼْﻤَﺔُ ﺃَﻣْﺮِﻱ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺩُﻧْﻴَﺎﻱَ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻣَﻌَﺎﺷِﻲ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺁﺧِﺮَﺗِﻲ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻣَﻌَﺎﺩِﻱ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻞِ ﺍﻟْﺤَﻴَﺎﺓَ ﺯِﻳَﺎﺩَﺓً ﻟِﻲ ﻓِﻲ ﻛُﻞِّ ﺧَﻴْﺮٍ، ﻭَﺍﺟْﻌَﻞِ ﺍﻟْﻤَﻮْﺕَ ﺭَﺍﺣَﺔً ﻟِﻲ ﻣِﻦْ ﻛُﻞِّ ﺷَﺮٍّ.* ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ، ﺑﺮﻗﻢ ۲٧۲۰ ._
*Allahumma Aslihlee deeniy Alladhee huwa Ismatu Amree, Wa Aslihlee Dunyayal latee feeha Ma’ashiy, Wa aslihlee aakhirateel Latee feeha Ma’aadee. Waj’alil hayata ziyadatan lee fee kulli Khayrin, Waj’alil Mauta rahatan lee min kulli sharrin*
_Ma'ana: *Ya Allah ka kyautata min addinina wanda shine cikamakin lamarina, Kuma ka kyautata min (lamarin) duniyata wacce acikinta ne rayuwata take. Kuma ka kyautata min (lamarin) lahirata wacce acikinta ne makomata take.Kuma ka sanya rayuwa ta zamto Qaruwa ce gareni acikin kowanne alkhairi. Kuma ka sanya mutuwa ta zamto hutu ce gareni daga dukkan sharri.*
_In shaa Allah idan ki ka riƙi wannan addu'ar za ki samu rangwame a al'amuranki na rayuwa._
_Sannan game da ƙwarjini, akwai abubuwan da za ki yi domin samunshi, kamar:_
_— Kyauta da kawaici, tare da kauda kai da rashin kwadayi._
_— Adalci da girmama mutane._
_— Hakuri da dogaro ga Allah tare da rashin hadama._
_— Rashin girman kai._
_— Yanke mu'amala da mutanen banza, ki guji duk wata ƙawa ko saurayin da bashi da ɗabi'a mai kyau._
_— Karban gyara da nasiha idan mutum yayi kuskure._
_— Jin tsoron Allah da kyautata ibada tare da tsare dokokin Allah._
_Idan har ki ka kiyaye waɗannan abubuwan, haƙiƙa ƙwarjininki da ƙauna zai ƙaru a zukatan al'umma, duk da ba kowane zai so ki ba, amma haƙiƙa Allah ze so ki domin kin kiyaye haƙƙoƙinSa, kuma duk wanda ya samu soyayyar Ubangiji, to haƙiƙa babu abin da ya rage masa._
_Wannan shi ne abin da zan iya cewa. Allah ne mafi sani._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_
Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.