INA DA LAIFI?

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum malam dan allah inada tambaya shin akwai laifi idan naroki allah yakaramin wani abu daga cikin irin halintar dayaimin nagode.

_*Amsa:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._

_'Yar uwa, ya na daga cikin ladubban yin addu'a, wato yin Koyi da Biyayya ga Annabi (ﷺ) a lokacin addu'a. Domin Allah (ﷻ) Yana cewa:_

*”وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُم تَهتَدُونَ“*

_Ma'ana: *“Ku bi shi, mai yiyuwa kun samu shiriya”* (Al-a'raf 158)_

_Saidai kuma, a gaskiya ni ban san wani nassi da ya zo cewa Manzon Allah (ﷺ), ko sahabbansa, ko wasu magabata na Kwarai na rokon Allah a kan ya kara masu wani abu daga surar jikinsu ba._

_Sannan, malamai suka ce, yana daga cikin sharuddan addu'a; kada mutum ya roki abin da a al'adance ba mai yiwuwa bane, ko ya sabawa dabi'a, Wanda kuma hakika tambayarki ta yi dai-dai da wannan qaulin._

_Duk wata halitta da Allahu (SWT) Ya yi, to akwai hikima a cikin hakan, ba wai don Allah ba ya son mutum bane yake yo shi gajera, ko dogo, baki ko mummuna, Aa, Shi Allah Ya na halitta ne yanda yake so ba yanda mutum ya so ba. Allah (ﷻ) Yã ce:_

_*”وَرَبُّكَ يَخلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَختَارُ مَا كَانَ لَهُمُ الخِيَرَةُ....“*_

_Ma'ana: *“Kuma Ubangijinka Ya na halittar abin da yake so ne kuma ya za6a, za6i bai kasance a gare su ba....”* (Al-Qasas: 68)_

_Don haka, a gaskiya a tamu fahimtar, bai halatta ki roki Allah Ya kara maki wata halittar jikinki wadda a al'adance ba bu wani tangarda a ciki, kamar ki ce Ya kara maki Kyau, Tsawo, Dogon hanci, ko wani abu makamancin hakan, wannan bai halatta ba._

_Amma idan wani abu ne wanda ya sa6a wa al'ada, wanda har ya kai ga za a iya kiransa da lalura, to wannan babu laifi ki roki Allah Ya kawo maki sassauci in shaa Allah._

_Wannan shi ne abin da na sani, Allah ne mafi sani._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Post a Comment (0)