*Jaruman Indiya 11 da suka Musulunta*
*1. AR Rahman*
An haife shi a matsayin wanda ke bin addinin Hindu, daga bisani kuma ya karbi musulunci.
Ya sauya sunansa daga Dileep zuwa Rahman. Mawakin Indiya ne wanda ya lashe kyautar Oscar. Mutum ne kuma da tunaninsa ya karkata zuwa kin wanzuwar Allah, da farko, amma daga baya sai ya karbi musulunci ya kuma zama mai karfaffan imani da Allah.
Abin da ya ce game da komawarsa musulunci ba abin mamaki ba ne kamar yadda ake nunawa.
"Mutanen gidanmu sun kadaita saboda haka lokacin da wasu karance-karance na Sufanci suka yi tasiri a kaina sai na musulunta".
Daga cikin wakokinsa da suka yi fice akwai Maa Tujhe Salaam.
*2. Kamala Surayya*
Ta fito ne daga cikin iyalai na kololuwa a kasar. Marubuciya ce, ta kuma musulunta ne a 1999. Ta sauya sunanta daga Madhavikkutty zuwa Kamala Surayya, bayan ta musulunta.
Ta musulunta ne bayan karanta wani littafi mai suna "The love Queen of Malabar''. Littafin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar.
*3. Dharmendra*
Shahararren jarumin fina-finan Bollywood, kuma mahaifin Sunny Deol, Bobby Deol, Esha Deol da Ahana Deol. Ko da yake ya karbi musulunci, amma majiyoyi sun ce ba ya dabbaka shi.
Dalilin musuluntarsa shi ne, saboda ya auri jaruma Hema Malini, a al'adarsu mabiya addinin Hindu, ba a auren mata biyu, to sai kuma soyayya ta shiga tsakaninsa da Hema har suka shirya auran juna a wancan lokacin, to sai ya duba ya ga ai addinin musulunci ya bayar da damar auren mata fiye da daya.
Sai ya musulunta, sannan suka yi aure tun a 1980. Ya fito a fina-finai kamar Sholay da Jugnu.
*4. Yuvan Shankar Raja*
Mawaki kuma mai rubuta waka. Da ne a wajen shahararren mawakin nan Ilayaraja. Bai jima da karbar musulunci ba. Shekarunsa a 2018, 38.
Ya bayyana dalilin da ya sa ya musulunta. Ya ce "Mahaifina rikakken mabiyin addinin Hindu ne, kuma ya yi nisa wajen camfe-camfe ta yadda ko da gilashi ne ya fashe sai ya kira malamin duba.
Dukkan iyayena sun yi imani da camfi, to wata rana sai mahaifiyata ta mutu a hannuna bayan gajeriyar rashin lafiya, nan na yi tunani na ce ya aka yi haka, yanzu fa take numfashi, to yaxun tana ina?
Anan na fahimci cewa ba wanda zai karbi numfashinta face Allah (SWA)".
5. Mamta Kulkarni
Ta taka muhimmiyar rawa a fina-finan Bollywood. Mijinta Vicky Goswami ya fara musulunta, da za ta aure shi, sai ta musulunta ita ma.
Yanzu haka suna zaune a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Ta fito a fina-finai kamar Karan Arjun da kuma Beqabu.
*6. Mahesh Bhatt*
Furodusa ne kuma daraktan fina-finan Bollywood. Ya musulunta ne saboda ya auri matarsa ta biyu Soni Razdan, kasancewar a addinin Hndu ba a auren mace fiye da guda.
To sai dai kuma rahotanni sun ce duk da ya musuluntan ba ya dabbaka addinin. Mahesh Bhatt, mahaifine ga jaruma Pooja Bhatt da Alia Bhatt. Daga cikin fina-finan da ya shirya akwai Gumrah da Duplicate.
7. Hema Malini
Shahararriyar jaruma ce a fina-finan Bollywood. Matar Dharmendra, mahaifiyar jaruma Esha Deol.
Hema sun yi aure da Dharmendra a 1980, amma kafin su yi aure sai da ta musulunta saboda mijin nata ma ya musulunta.
To amma Hema, har yanzu ta na bin addinin Hindu ne. Hema ta fito a fina-finai kamar Dream Girl da kuma Seeta Aur Geeta.
*8. Sharmila Tagore*
Sharmila Tagore, ta musulunta ne sakamakon auran mijinta Mansoor Ali Khan a shekarar 1969.
Ta sauya sunanta daga Sharmila Tagore zuwa Ayesha Sultana bayan musuluntarta.
Ita da mijinta, sun haifi 'ya'ya uku, Saif Ali Khan da Saba Ali Khan da kuma Soha Ali Khan.
Sharmila Tagore ta fito a fina-finan Bollywood da dama da suka yi fice kamar Aradhana wanda suka fito tare da Rajesh Khanna.
*9. Monica*
Fitacciyar jaruma ce a fina-finan kudancin India. Ta sanar da Musuluntarta ne a 2014, amma tun a 2010 ta karbi Musulunci. Ta sauya sunanta zuwa MG Rehima.
Mahaifinta Hindu ne, mahaifiyarta kuma kirista ce.
*10. Amrita Singh*
Amrita Singh ta taka muhimmiyar rawa a fina-finan Indiya. Tsohuwar matar Saif Ali Khan ce inda suka haifi 'ya'ya biyu, wato Sara Ali Khan da Ibrahim Ali Khan.
Ta taso a matsayin mai bin addinin Sikh daga bisani ta Musulunta. Cikin fina-finanta da suka yi tashe akwai Mard da Aaina
*11. Hans Raj Hans*
Hans Raj Hans, mawaki ne a Indiya. Ya musulunta ne a lokacin da ya ke kan
hanyarsa ta zuwa Pakistan.
A da yana bin addinin Sikh ne, daga bisani kuma ya Musulunta.
Tags:
Labarai (News)