JININ HAILA

_*Tambaya:*_

Assalamu Alaikum

Barka da warhaka

Don Allah inatambayane dan neman karin bayani akan jinin haila
Wato yanayin daukewansa
Saboda wani lokacin mutun zaiyi tsarki watau jinin ya dauke sai kuma ba gobe ko jibi sai ya da wo kadan kadan haka(baiku bata jiki)
Don Allah anan ya hukuncin yake??

_*Amsa:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._

_Abin da za ki yi shi ne, za ki kirga gwargwadon kwanakin al'adarki, ki bar Sallah da azumi, ki ba wa kanki hukuncin mai haila. Idan kwanakin al'adarki sun kare, sai ki yi wanka, ki ci gaba da al'amuranki, ki dauki jinin da ya ci gaba da zuba jinin rashin lafiya, kuma hukuncin mai jinin rashin  lafiya kamar hukuncin mai tsarki ne, idan za ki yi sallah sai ki yi tsarki, ki wanke jinin._

_Idan kuma ya zamana ba ki da al'ada sananniya, amma kina iya bambance jinin naki, to a wannan halin sai ki dauki jinin mai sifar haila a matsayin jinin haila, sai ki bar Sallah da azumi. 'Daya jinin kuma sai ki dauke shi jinin rashin lafiya ne. Ki yi wanka yayin da jinin da yake da sifar na haila ya dauke, ki ci gaba da ibadunki._

_Idan kuma ba ki da al'ada sananniya, kuma babu wata sifa da za ki bambance tsakanin jinin haila da wanda ba na haila ba, to a nan sai ki zauna iya kwanakin da galibin haila yake kasancewa, wato kwana shida ko bakwai a kowane wata; domin wannan itace galibin al'adar mata._

_Don haka 'yar uwa, da Wadannan halayen za ki yi amfani don gane matsayin hailarki._

Wallahu a'lamu.

_Dalibin ku:_

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Post a Comment (0)